30/04/2025
Majalisar Dokokin jihar Zamfara ta rusa kwamitoci, data zarga da almundahana.
A yau ne ɓangaren Majalisar Dokoki na Jihar Zamfara ya sanar da rushe dukkan shugabannin majalisar da kwamitocin, tare da kafa kwamitoci biyu masu muhimmanci domin sake tsara aikin majalisar bisa gaskiya da tsari.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Shugaban Majalisar na ɓangaren, Hon. Bashar Aliyu Gummi, bayan zaman majalisa da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa an sake kafa kwamitoci guda biyu masu muhimmanci – wato Kwamiti na Ladubba da ’Yanci da kuma Kwamiti na Ayyuka da Ababen More Rayuwa – wadanda za su kasance ƙarƙashin jagorancin Hon. Masama da Hon. Bashir Sarkin Zango daga yau.
Majalisar ta bayyana aniyar ta ta kai rahoton duk wata almundahana da tsofaffin shugabannin majalisar s**a aikata zuwa hukumar EFCC da ICPC domin dawo da duk kudaden jama’a da aka karkatar.
A yayin zaman, ƙarƙashin batutuwa na gaggawa da s**a shafi bukatun jama’a, ‘yan majalisar sun yi tir da yadda gwamnatin Dauda Lawal ke bai wa wasu ƙananan hukumomi fifiko wajen naɗa sakatarorin dindindin, inda wasu yankuna ba su samu ko guda ba.
A cikin kudurin da Hon. Ibrahim Tudu Tukur, dan majalisa mai wakiltar gundumar Bakura ya gabatar, ya jaddada yadda wasu ƙananan hukumomi irin su Tsafe, Maradun da Birnin Magaji ba su samu naɗin sakatare dindindin ko guda ba, yayin da wasu yankuna s**a samu fiye da tara.
Ya bayyana cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, kuma dole ne a gyara wannan al’amari domin tabbatar da adalci da daidaito ga kowa a jihar.
Majalisar ta umurci Gwamna Dauda Lawal da ya soke nadin kuma ya sake duba batun cikin adalci domin a bai wa dukkan ƙananan hukumomi wakilci.
Haka kuma, majalisar ta nuna damuwa kan jinkirin da ke cikin aikin hanya mai tsada ta Gusau-Dansadau da aka riga aka biya kwangila tun bara, amma ba a gama ko kilomita biyar ba.
Saboda haka, majalisar ta gayyaci kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar da ya bayyana a gaban ta don ya bayyana dalilin tsaikon aikin, inda s**a jaddada cewa “duk kuɗin jama’a da na haraji dole ne a yi amfani da su cikin gaskiya kan abin da aka tsara.”
Majalisar ta kuma bukaci Gwamna Dauda Lawal da ya buɗe aƙalla makarantun kwana biyu daga kowanne yankin Sanata guda uku na jihar, wadanda aka rufe saboda rashin tsaro, k**ar yadda iyaye s**a bukata. Majalisar ta zargi gwamnati da kin buɗe makarantu ne domin guje wa aiwatar da shirin ciyar da ɗalibai wanda ke taimaka wa yara ‘yan ƙasa marasa ƙarfi da kuma rage barin zuwa makaranta ga yara.
A wani ɓangaren majalisar dokoki ta jihar ya fito makon da ya gabata ƙarƙashin jagorancin Hon. Gummi, inda s**a fara magana kan muhimman batutuwa da s**a shafi jama’a da s**a hada da s**a ga gwamnatin jihar da kuma majalisar ɓangaren Hon. Moriki, wadda ita da gwamnatin ba su bayyana matsayinsu ba a fili.