Nani Tv News

Nani Tv News Artist
Musical��
Graphics
Editor
Proudly Muslims~��
Twitter zaharadeensani1
Do contact us on�
wh

Mataimakin babban kwamandan Hisba Dakta Mujahid Aminuddeen ya bayyana hakan ne, yayin tattaunawa da Premier Radio.Ya ce ...
17/08/2025

Mataimakin babban kwamandan Hisba Dakta Mujahid Aminuddeen ya bayyana hakan ne, yayin tattaunawa da Premier Radio.

Ya ce hukumar tana taka gagarumar rawa wajen magance matsalolin aure.

Ya kuke kallon wannan kalamai na mataimakin shugaban hukumar Hisba?

Ruwan ƙanƙara ya lalata gonaki a gundumar Damagaram Takaya, jihar Zinder.Gonakin da ke Alberkaram, Birji Zomo, Angoual D...
17/08/2025

Ruwan ƙanƙara ya lalata gonaki a
gundumar Damagaram Takaya, jihar Zinder.

Gonakin da ke Alberkaram, Birji Zomo, Angoual Dilla, Garin Hadjia, Garin Halilou, Tchidassaoura har zuwa Garin Koublé sun lalace gaba ɗaya.

Kwamishinan Sufuri Na Jahar Oyo Prof. Raphael Ofanja Ya karbi Addinin Musulunci.Tsohon Komishinan Sufuri na Jihar Oyo Fa...
17/08/2025

Kwamishinan Sufuri Na Jahar Oyo Prof. Raphael Ofanja Ya karbi Addinin Musulunci.

Tsohon Komishinan Sufuri na Jihar Oyo Farfesa Raphael Afonja , ya karbi addinin Musulunci, ya sauya suna daga Raphael zuwa Abdurrahman.

Allah Ya Yiwa Babban Basarake Arewacin Najeriya Sarkin Zuru Muhammad Sani Sami Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi A Mulkin Soja...
17/08/2025

Allah Ya Yiwa Babban Basarake Arewacin Najeriya Sarkin Zuru Muhammad Sani Sami Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi A Mulkin Soja, Rasuwa A Wata A Asibiti Da Ke Birnin Landan A Safiyar Ranar Lahadi.

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Cika Shekaru 84 A Yau LahadiGa wasu daga cikin ayyukan cigaban da ya kawowa Nij...
17/08/2025

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Cika Shekaru 84 A Yau Lahadi

Ga wasu daga cikin ayyukan cigaban da ya kawowa Nijeriya;

Shi ya kirkiri Jihar Yobe

Shi ya kirkiri Jihar Katsina

Shi ya kirkiri Jihar Taraba

Shi ya kirkiri Jihar Jigawa

Shi ya kirkiri Jihar Kebbi

Shi ya kirkiri Jihar Enugu

Shi ya kirkiri Jihar Edo

Shi ya kirkiri Jihar Delta

Shi ya kirkiri Jihar Osun

Shi ya kirkiri Jihar Akwa Ibom

Shi ya kafa FRSC

Shi ya kafa SSS

Shi ya kafa NIA

Shi ya kafa DIA

Shi ya gina A*o Rock Villa

Shi ya gina Third Mainland Bridge

Ya kammala Shiroro Power Station

Ya gina Toja Bridge Kebbi

Ya ƙirƙiri Jibia Water Plant

Ya gina Challawa Cenga Dam Kano

Hanyar Kano–Abuja dual carriageway

Madatsar ruwa a Kano

Sauran ayyuka sun haɗa da:
1.Hedkwatar ECOWAS Abuja
2.Cibiyar taro ta kasa da kasa Abuja
3.Gidajen FHA a duk faɗin ƙasa
4.Kotunan koli a jihohi
5.Ma’aikatar Tarayya a jihohi 36/Abuja
6.Ofisoshin jam’iyya 2 a jihohi 36
7.Hedkwatar rassa 4 na sojojin ƙasa
8.Barikin sojoji Abuja
9.Makarantar Sojojin Tanki Bauchi
10.Makarantar Sojojin Ruwa Calabar
11.Gidaje ga GOCs 4
12.Navy Dockyard
13.Dockyard Snake Island
14.Gidaje ga ma’aikatan ayyuka da gidaje
15.Gwagwalada/Isheri/Prototype housing
16.Hedkwatar FEPA Abuja
17.Ofisoshin FEPA da lab. Yaba
18.National Eye Centre Kaduna
19.Aluminium Smelter Ikot Abasi
20.Kotun Koli Abuja
21.Ajaokuta Steel Project
22.Filin jirgin sama Abuja Ph1&2
23.Majalisar Tarayya Abuja
24.Fadar Shugaba Abuja
25.Hedkwatar NIA
26.Hedkwatar SSS Abuja
27.Bankin Lamuni FMBN Lagos
28.Rassa FMBN ƙasa baki ɗaya
29.CBN Hqrts Abuja
30.Minting/Security Abuja
31.Jabi District Abuja
32.Central Area Ph1&2
33.A*okoro Area
34.Garki Ph1,2,3
35.Gudu District
36.A*okoro SW Extension1&2
37.Maaikatu jihohi 1991
38.Majalisar dokoki jihohi 1991
39.Shari’a Buildings jihohi 1991
40.Asibitin Maitama Abuja
41.Asibitin Wuse Abuja
42.Asibitin Fadar Shugaba
43.Asibitoci a jihohi
44.Ruwan sha Gusau
45.Ruwan sha A*okoro
46.Ruwan sha Kubwa
47.Ruwan sha Abuja Municipal

The APC candidate in the August 16 bye-election in Ibadan North Federal Constituency, Adewale Olatunji, has lost his pol...
17/08/2025

The APC candidate in the August 16 bye-election in Ibadan North Federal Constituency, Adewale Olatunji, has lost his polling unit to another party. The ADC candidate in the election has also raised an alarm. Details in the comments

Photo credit: X/

17/08/2025

Dalilin da ya sa zaɓen cike gurbi na jihar Zamfara ya zama 'inconclusive' - Hukumar INEC

Ba Sulhu Tsakanin Mu Da 'Yan Bindiga, Inji Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Gwamnan ya bayyana haka ne a daidai lokacinda ake...
17/08/2025

Ba Sulhu Tsakanin Mu Da 'Yan Bindiga, Inji Gwamnan Zamfara Dauda Lawal

Gwamnan ya bayyana haka ne a daidai lokacinda ake raɗe-raɗin cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji na neman ayi sulhu.

Me za ku ce?

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Sani Dahiru Umar na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen ...
17/08/2025

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Sani Dahiru Umar na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Basawa a majalisar dokokin jihar Kaduna.

Da yake bayyana sak**akon zaɓen, Farfesa Nasiru Rabi’u daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya sanar da cewa ɗan takarar APC ya samu kuri’u 10,926, inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mu’azu Salisu Danyaro, wanda ya samu kuri’u 5,499.

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi a jihar Jigawa, a kananan hukumomin Babura da Garki da gagarumin r...
17/08/2025

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi a jihar Jigawa, a kananan hukumomin Babura da Garki da gagarumin rinjaye.

APC 38,449
PDP 13,519
NNPP 2,931

🔴 Shugaban Faransa immanuel macron ya bukaci a gaggauta sakin ɗan ƙasar ta da aka k**a, wanda ake zargin hannu a yunkuri...
17/08/2025

🔴 Shugaban Faransa immanuel macron ya bukaci a gaggauta sakin ɗan ƙasar ta da aka k**a, wanda ake zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Bamako. Ya jaddada cewa Faransa ba ta da hannu a wannan al’amari.

Address

Tudun Wada Gusau Premir Road
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nani Tv News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Nani Tv News:

Share