Mal Abubakar ibn taimiyya tsaunee Gusau

Mal Abubakar ibn taimiyya tsaunee Gusau Insha Allah wannan page zashi taalaqa gurin kawo maku karatu d ilimoma na addinin musulunchi

26/08/2024

Alhamdulillah

Bansan Wace Irin Giya Yan Shi’a Ke Sha Ba.Mutuwar shugaban ƙasar Iran 🇮🇷 babu shahada acikin ta, duk wanda ke zagin saha...
21/05/2024

Bansan Wace Irin Giya Yan Shi’a Ke Sha Ba.

Mutuwar shugaban ƙasar Iran 🇮🇷 babu shahada acikin ta, duk wanda ke zagin sahabban annabi saw, yake ƙaryata hadissan annabi saw, yake la’antar matan gidan annabi, to wannan mutumin karku ɓatawa kanku lokaci yimasa addu’a bayan mutuwarsa.

Wannan mutumin bazayyi shahada ba. Da kuyi masa addu’ar neman gafara, gwanda kuyi mining cryptocurrency yafi alkhairi agareku.

Sai ka kai oga awurin zagin sahabbai da la’antar sahabbai, da ƙaryata hadissan annabi saw, da juye ma’anar ayoyin alkur’ani maigirma sannan ne za’a ɗoraka akan kujerar shugabancin ƙasar Iran 🇮🇷

Saboda haka, karku yaudare kanku (Ibrahim Raisi) ba shahidi bane, kuma zaije ya tararda tsiyar da ya shuka anan duniya.

Allah ya ƙara kare al’ummar annabi daga shi’a da sharrin shi’a da makircin shi’a da bala’in shi’a

Ameen

Alhassan Mai Lafia

Dogaro Ga Allah (SWT)1. Umarni da dogaro ga Allah da yabon masu dogaro ya maimatu a cikin Alƙur'ani a wurare da yawa, ki...
20/05/2024

Dogaro Ga Allah (SWT)

1. Umarni da dogaro ga Allah da yabon masu dogaro ya maimatu a cikin Alƙur'ani a wurare da yawa, kimanin wuri (70). Wannan yana nuna mana girman mahimmancin wannan ibada ta dogaro ga Allah (SWT).

2. Allah (SWT) ya cancanci a dogara gare shi, saboda siffantuwarsa da duk siffofi na kamala, kamar cikar iliminsa da yalwar rahamarsa da cikar ƙudurarsa da buwayar mulkinsa, da kyakkyawar hikimarsa da sauransu.

3. Babu wanda ya kai annabawan Allah dogaro ga Mahaliccinsu cikin dukkan al'amuran rayuwarsu, wannan ya sa nasarar Allah ta zamo tare da su a koyaushe. S**a zamo abin koyi ga 'yan baya, ababen alfahari ga mutanen kiriki.

4. Bawa yakan dogara da Mahaliccinsa saboda ya yi imani da shi, ya kuma yi imani da ƙadarrarsa, tare kyautata zato a gare shi koyaushe.

5. Dogarar bawa ga Allah (SWT) ba za ta cika ba, sai tare da cikakken kyautata zato ga Allah (SWT). Bawa ya yi imani cewa, Allah (SWT) mai taimakonsa ne matuƙar ya kasance mai gaskiya wajen tsayuwa da umarninsa da kiyaye dokokinsa da yarda da kyakkyawan zaɓinsa. Idan zaton bawa ga Ubangijinsa ya munana, to a kan rasa dogaro da Allah a tare da shi.

6. Duk mai dogaro ga Allah (SWT) zai cimma manyan nasarori a ruyarsa kamar haka:

• Samun soyayyar Allah a gare shi.
• Dacewa da kulawar Ubangijinsa a gare shi.
• Kuɓuta daga wulaƙanta ta tozarta a duniya da lahira.
• Kuɓuta daga makircin Shaiɗan da sharrinsa.
• Kuɓuta daga damuwa da ɓacin rai.
• Kuɓuta daga azabar Allah da kamunsa mai tsanani.
• Samun shiga gidan Aljanna.

TSAKANIN IBADA DA AL'ADA 1. Duk wani tasaruffi na ɗan'adam a maganganunsa da ayyukansu bai wuce iri biyu ba:Na ɗaya, Iba...
19/05/2024

TSAKANIN IBADA DA AL'ADA

1. Duk wani tasaruffi na ɗan'adam a maganganunsa da ayyukansu bai wuce iri biyu ba:

Na ɗaya, Ibadu, waɗanda su ne addininsa.

Na biyu, al'adu, waɗanda su ne gudanar da mu'amalolin rayuwarsa ta yau da kullum.

2. Binciken ƙwaƙwaf a cikin ƙa'idoji na shari'ar Muslunci ya tabbatar da cewa, duk wata ibada ba za ta tabbata ba sai ta hanyar shari'a kaɗai.

3. Amma al'adu na rayuwar mutane ta yau da kullum, shari'a ta nuna cewa, babu abin da ake haramta musu daga ciki sai abin da Allah shi da kansa ya haramta.

4. Domin umarni da hani su ne shari'ar Allah. Ibada kuwa dole ne ta zamanto abin da aka yi umarni da aikta shi. Duk abin da bai tabbata ba ta hanyar umarnin Allah da Manzonsa, to ta yaya zai zama shari'ar Allah?

5. Hakanan duk wata al'ada da shari'a ba ta yi hani a kanta ba, to ba za a yi mata hukunci da haramun ba.

6. Saboda haka ne Imamu Ahmad da sauran malaman hadisi suke cewa: ƙa'ida dangane da ibada ita ce, sai an samu nassi daga Allah ko Manzonsa. Ba za a ɗauki wani abu a matsayin addini ba har sai da izinin Allah, idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ko dai suna da wasu abokan tarayya ne da s**a shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izinin yin sa ba?..) [Shura, aya ta 21].

7. Hakanan kuma ƙa'ida game da al'adu ita ce, an yi afuwa da rangwame, ba za a haramta wata al'ada ba sai wadda Allah (SAW) da kansa ya haramta. Idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”..) [Yunus, aya ta 59].
[Duba, Ibn Taimiyya, Majmu'ul Fatawa, juzu'i na 29, Shafi na 16-17].

16/05/2024
16/05/2024

Masha Allah godiya t tabbata GA Allah s w a

16/05/2024

Gusau is a city and Local Government Area located in northwestern Nigeria. It is the capital of Zamfara State.

Address

Tudun Wada Gudau
Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mal Abubakar ibn taimiyya tsaunee Gusau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share