DOKIN KARFE Online TV

DOKIN KARFE Online TV fadakarwa, Nishaɗantarwa ,tareda labarai nagaskiya

🌟 A Tribute to a Visionary Leader 🌟Umar Alfuntawy Imam Dr. Umar Aminu Imam MPH, PhD.Provost, Muslim Community College of...
24/07/2025

🌟 A Tribute to a Visionary Leader 🌟
Umar Alfuntawy Imam
Dr. Umar Aminu Imam MPH, PhD.
Provost, Muslim Community College of Health Science and Technology, Funtua, Katsina State
In a world yearning for true leadership, Dr. Umar Aminu Imam stands tall as a symbol of excellence, humility, and purpose.
As Provost of the Muslim Community College of Health Science and Technology, Funtua, he has not only led with wisdom but transformed the institution into a center of distinction and innovation.

A Public Health expert, a passionate Environmentalist, and an influential Public Speaker, Dr. Imam is widely respected for his dedication to both Islamic and modern knowledge, empowering students and youth to thrive in all spheres of life.

With uncountable achievements, numerous honors and awards, and a legacy of good governance, he exemplifies what it means to serve with integrity. His leadership is marked by humility, discipline, and a visionary spirit that inspires all who cross his path.

Through his courageous voice, he encourages students to pursue excellence, serve humanity, and uphold both faith and professionalism.

May his legacy continue to grow, and may Allah (SWT) reward his service to education, health, and the Muslim Ummah.

Allah ya yiwa tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari Tasuwa yau Lahadi.Allah yajikansa da rahama
13/07/2025

Allah ya yiwa tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari Tasuwa yau Lahadi.
Allah yajikansa da rahama

The strength of a man is in his ability to think of how to solve problems. May Allah provide for all men to meet their r...
08/07/2025

The strength of a man is in his ability to think of how to solve problems.

May Allah provide for all men to meet their responsibilities. Amin ya Hayyu ya Qayyum 🙏

Gargadi Gargadi GargadiNa Ƙarar Da Budurci na T**i a Banza ina Da Saurayi Mun Kai Shekara Goma  Dashi Kullum Yana yawan ...
08/07/2025

Gargadi Gargadi Gargadi

Na Ƙarar Da Budurci na T**i a Banza

ina Da Saurayi Mun Kai Shekara Goma Dashi Kullum Yana yawan Taɓa jikina Har yakai yakawo Muna zuwan hotel Dashi yayi wasa Dani yadda yakeso...

Bayan haka yayi Alkawarin Zai Aure ni Daga baya naji labarin yayi Aure ban Nunamishi na San yayi aure ba Kuma still Yana bibiyata wai mutafi hotel

Bayan da Auren shi Kullum sai Yana kirana a waya ya Ringa ce min mu tafi hotel Abin yanzu yana matukar damu na. amma nasan ba komai bane

ya ya jawo min hakan ba sai son Abin Duniya sabida duk lokacin da na yake shawarar na rabu dashi sai na fara tunanin irin ƙuɗin da yake bani sai naji ba zan iya Rabuwa dashi ba

Babbar matsalar ma a yanzu ga shi Shekaru sun fara cin min na karar da Budurci na a T**i bu kuɗin da yake bani kuma shi ma yanzu ya daina kula ni

A Karshe ina kira yan uwa mata su dauki Darasi akan abinda ya faru dani sannan a kula da samari yan karya masu kashe zuciyar yan mata daci kudi

Zuciyata cike dake da Nadama yanzu waca shawara zaku bani

Gani Gawane Coppy

FAHIMTA FUSKAWata mata da aka aura ta je wurin wani malamin tana kuka sosai, tana korafin yadda mijinta ke cin mutumci d...
07/07/2025

FAHIMTA FUSKA
Wata mata da aka aura ta je wurin wani malamin tana kuka sosai, tana korafin yadda mijinta ke cin mutumci da zarafinta.

"Malami," ta fara, "babu abin da ban yi don faranta masa rai ba. Ina dafa masa abinci akan lokaci, ina wanke masa kaya, ina kula da yara da gida sosai. Amma duk da haka sai ya dinga dukan ni. Ba zan iya yin magana a gidan ba. Na gaji."

Malamin ya yi mata addu’a sannan ya ba ta ƙananan duwatsu guda uku.

"Ga wannan," inji shi, "duk lokacin da mijinki ya fusata, ki sa su a bakinki. Ki tabbatar ba ki ce komai ba ko da kuwa ya yi miki ba daidai ba. Idan kika yi haka yadda na umarce ki, za ki ga mijinki zai canza miki sosai."

Matar ta gode wa malamin kuma ta tafi. Da mijinta ya dawo gida washegari, sai ya fara korafi k**ar yadda ya saba, amma sai mamakinsa ya ga matarsa ba ta ce uffan ba. Ta ci gaba da aikinta a gidan k**ar yadda aka saba.

Washegari, sai mijin ya sake zuwa da fushi da zagi, amma matar ba ta ce komai ba. Ta cigaba da aikinta yadda ya k**ata.

A rana ta uku, mijin ya dawo gida, ya kira matarsa karo na farko cikin dogon lokaci.

"Ke, na siya miki wasu kaya a hanya daga aiki yau. Na san za su miki dadi."

Amma matar ba ta ce komai ba. Ta karɓi kyautar tana kuka. Har yanzu ba ta yi magana ba. Sai mijin ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, ya ce,
"Na sani ban kyauta miki ba. Ki yafe ni. Zan fara kula da ke k**ar sarauniya daga yau. Ina son ki."

"Ina son ka ma, mijina," matar ta amsa.

Ta kasa gaskanta abin da kunnenta ke ji. Mijinta ya canza k**ar yadda malamin ya faɗa.

Ta koma wurin malamin domin bayyana farin cikinta.
"Malami, na yi farin ciki! Mijina ya canza gaba ɗaya! Wadancan duwatsun da ka bani sun yi aiki!"

Malamin ya kalle ta, ya murmusa ya ce,
"Duwatsun ba su da wani sihiri k**ar yadda k**e tunani. Mijinki yana da matsalar fushi, kuma ke kina da bakin zaki. Idan na ce miki kawai ki daina maida masa martani lokacin da ya fusata, da wuya ki iya. Shi yasa na baki duwatsun don su hana ki magana."

Matar ta murmusa, "Haka kawai kenan?"

"Eh," inji malamin. "Ki koma gida, ki ci gaba da abin da kika koya. Allah ya albarkaci gidanku!"

06/07/2025

Labaran Safiyar Lahadi 11/01/1446AH - 06/07/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi baƙi mazauna Najeriya kan sabunta izinin zamansu ko fuskantar hukunci.

Mai magana da yawun majalisa yace bazasu dawo da Sanata Natasha ba har sai ta baiwa Majalisa hakuri.

Mutane 7 sun rasa rayukan su a wani mummunan hatsarin mota akan hanyar Alkaleri zuwa Gombe.

Jita jita ta fara ƙarfi cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin ficewa jam’iyyar APC zuwa ADC.

Malaman Jami'ar Jos sun shiga yajin aiki.

Ƴan sanda sun tarwatsa masu safarar mutane tare da ceto mutane 40 a jihar Ondo.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bullar cutar amai da gudawa a makarantar sikandire dake anguwar Kawo dake jihar.

Wasu ƙungiyoyin mata aƙauyukan Bendeghe Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi barazanar gudanar da zanga zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba.

Allah Ya yi wa fitaccen mai yabon Annabi Muhammad SAW, Abdullahi Shehu Gano wanda aka fi sani da Dangano mai waƙar ‘Saba'a’ rasuwa.

Sojojin Ukraine sun k**a wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu.

Jirgin farko na 'yan ciranin da Trump ya kora sun isa Sudan ta Kudu.

Dakarun sojin Nijar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 41 a yayin wasu tagwayen hare-hare da aka kai musu kan iyakar Burkina Faso da Mali.

Isra'ila ta amincewa tattaunawa a Doha bayan ta yi watsi da buƙatun Hamas.

Juventus na ƙara ƙaimi a ƙoƙarin ɗauko Sancho daga Manchester United kuma tana iya yin tayin musaya da ɗan wasanta Douglas Luiz.

Ɗanwasan Manchester United Rashford da takwaransa na Manchester City Jack Grealish na iya samun damar barin ƙungiyoyinsu kan fam miliyan 40 kowannen su a wannan bazarar.

Barcelona ta shirya tattaunawa da Manchester United a ƴan kwanaki masu zuwa game da yarjejeniyar sayen Rashford a matsayin aro.

Chelsea ta shaida wa Manchester United cewa sai ta biya fam miliyan 35 idan suna son ɗaukan Christopher Nkunku.

Ɗanwasan Tottenham Heung-min Song ya shirya ya yi watsi da komawa Los Angeles FC duk da cewa ya bayyana ƙudirinsa na barin Tottenham a wannan bazarar.

Ministan na Abuja Nyesom Wike ya ce Allah ne ya ceci Najeriya da ya kawo shugaba Tinubu saboda kaɗan ya rage a binne ƙas...
06/07/2025

Ministan na Abuja Nyesom Wike ya ce Allah ne ya ceci Najeriya da ya kawo shugaba Tinubu saboda kaɗan ya rage a binne ƙasar.

Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai tsaya takara a 2027 ba.
06/07/2025

Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai tsaya takara a 2027 ba.

Gwamnonin PDP Biyar na Shirin Shiga Jam’iyyar ADCWata majiya mai ƙarfi daga jam’iyyar ADC ta bayyana cewa akwai yiwuwar ...
05/07/2025

Gwamnonin PDP Biyar na Shirin Shiga Jam’iyyar ADC

Wata majiya mai ƙarfi daga jam’iyyar ADC ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu gwamnoni biyar na jam’iyyar PDP su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

Majiyar, wanda tsohon sanata ne daga jihar Katsina, ya ce, Gwamnonin PDP guda biyar sun ba mu tabbacin cewa za su shigo ADC. Sai dai suna jiran a ga ƙarshen fitinar Wike a cikin PDP. Muna sa ran haɗuwa da su bayan taron gangamin jam’iyyar na gaba domin nazari da yanke matsaya.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin gwamnoni, har da na jam’iyyar APC, na goyon bayan ƙungiyar hadakar data kafa ADC, tun watanni 18 da s**a wuce muka fara shirya wannan haɗin gwiwar.

Wasu gwamnoni daga APC an tuntuɓe su kusan shekara guda da ta wuce. Sun amince da mu, amma ba zan bayyana sunayensu ba, inji majiyar.

22/06/2025
22/06/2025

Gaskiyar Lamari

Address

Mada, Kwaren Auta
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DOKIN KARFE Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DOKIN KARFE Online TV:

Share

Category