31/08/2026
QAFILATUL MAHABBA ISLAMIC FOUNDATION OF NIGERIA
Reshen Gusau, Jihar Zamfara
SHAH'RU RAHMA 2026
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Qafilatul Mahabba Islamic Foundation of Nigeria, Reshen Gusau, Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Jagoranmu mai albarka, Sheikh Prof. Ibrahim Maqari, Chief Imam na National Mosque Abuja.
Ta gudanar da taron raba tallafin watan Rabi'ul Auwal (Shahrur Rahmah), watan haihuwar Annabi Muhammad (SAW), cikin nasara da yardar Allah.
Wanda jagora kuma shugaba na wannan gidauniya na kasa reshen Jihar Zamfara, Sheikh Dr. Saminu Dalhat Ahmad ya jagoranta.
Wanda ya Gudana A jiya Laraba 17_Rabi'ul Awwal_1448 Dai Dai da 30/08/2026
A Makarantar Azzahra, Unguwar Yarima, Gusau, Jihar Zamfara.
Da 10:00 na safe.
A cikin wannan taro mai albarka, an gudanar da ayyukan alkhairi kamar haka:
1. Ciyar da mabukata abinci dafaffe tare da nama.
2. Raba kayan abinci ga mabukata.
3. Raba fom ɗin rajista ga waɗanda za a koyar da sana'o'i (Entrepreneurship).
4. Ɗaukar nauyin karatun 'ya'yan marayu na matakin Firamare da Sakandare.
5. Yanka shanu tare da rabon naman ga mabukata.
6. Ziyartar asibiti domin tallafa wa marasa lafiya.
7. Raba littafin Tambayoyin Addinin Musulunci – Kashi na Biyu, wanda Sheikh Ibrahim Ahmad Makari ya wallafa.
8. Raba kwafe-kwafen Alƙur'ani Mai Girma ga ɗaliban makarantu da s**a halarci taron.
Muna miƙa godiya ta musamman ga:
- Jagoranmu, Sheikh Prof. Ibrahim Ahmad Makari, bisa jagoranci nagari da ci gaba da bayar da goyon baya.
- Jagoran wannan na jihar zamfara Dr. Samin Dalhat Ahmad
- Dukkan masu bayar da tallafi da gudummawa da s**a ba da tasu gudunmawar wajen nasarar wannan aiki.
- Kwamitin gudanarwa na Reshen Gusau da dukkan masu aikin sakai.
- Babban baƙon mai jawabi, Dr. Nasir Sheikh Balarabe Gusau.
- Dukkan 'yan'uwa Musulmi da s**a halarta tare da addu'o'insu.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi wannan aiki a matsayin Sadakatul Jariya, Ya sanya shi cikin ayyukan alheri masu ɗorewa, Ya saka wa duk wanda ya ba da gudunmawa da mafificin alheri, Ya ƙara mana haɗin kai, soyayya da zaman lafiya domin cigaban addini da al'umma.
«"Wa mā tunfiqū min shay'in fī sabīlillāhi yuwaffa ilaykum wa antum lā tuẓlamūn."»
Allah (SWT) Ya ƙara mana ikon ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyukan alheri. Amin.