
23/08/2025
Masarautun Hausawa da Ba a Ci da Yaki ba a Lokacin Jihadin 1804
Lokacin Jihadin Shehu Usman ɗan Fodio a ƙarni na 19, duk da girman tasirinsa, ba dukkan masarautun Hausawa aka ci su da yaki ba. Wasu sun tsira ta hanyar hijira da sauya cibiyar mulki, wasu kuma nisan wuri, hikima, ko matsayar shugabanni sun hana jihadin ya shafe su. Wannan bayani na kawo jerin waɗannan masarautu tare da takaitaccen bayani kan yadda s**a tsira.
I. Masarautun da S**a Yi Hijira ko S**a Gusa Daula:
1. Gobir
– Bayan faduwar Alkalawa, masarautar ta koma Tsibiri da Sabon Birni, inda sarauta ta ci gaba.
2. Zamfara
– Bayan rushewar daula, Hausawan Zamfara s**a watse s**a kafa sababbin masarautu k**ar:
Anka
Mafara
Bakura
Bukkuyum
Gumi
Tsafe
Kwatarkwashi
3. Katsina
– Sarautar ta koma Maradi (a Jamhuriyar Nijar), inda ta ci gaba da wanzuwa bayan faduwar Birnin Katsina.
4. Zazzau
– Bayan shan kaye a Zariya, sarakunan Zazzau s**a kafa sabuwar cibiyar mulki a Suleja (wanda ake kira "Zazzau Suleja").
5. Hadejia
– Sarkin Hadejia ya janye ba tare da fada ba, ya miƙa mulki cikin salama ga Fulanin jihadi. Ya ɓoye kansa don kauce wa zubar da jinin talakawansa, yana mai cewa “mulkin suke so, to gashi nan.”
6. Azare
– Mai mulkin ya miƙa mulki da hikima, don kare rayukan jama’a daga bala’in yaki.
7. Kebbi
– Masarautar ta koma daga Kabi zuwa Argungu, inda s**a kafa sabuwar cibiyar mulki.
8. Daura kuma s**a kafa Zangon Daura
II. Masarautun da Jihadin Bai Shafa ba Ko S**a Tsira Saboda Nisan Wuri Ko Hikima:
1. Agadez (Nijar)
– Tsohuwar daula ce tun ƙarni na 14, haɗakar Berber da Hausawa. Ta kauce wa jihadi saboda nisan wuri da tsarin mulkinta mai zaman kansa.
2. Tessaoua (Tasawa)
– Masarauta a Nijar da ke gefen yammacin Katsina, ta tsira daga jihadi.
3. Damagaram
– Masarautar Larabawa da Hausawa da aka kafa a ƙarni na 17. Da fari suna ƙarƙashin umarnin Borno, amma daga bisani s**a ɓalle a ƙarni na 19.
4. Adar
– Ƙaramar masarauta a Nijar da ke tsakanin Damagaram da Tessaoua, ba ta fuskanci ji