21/10/2025
Muna yaba wa Minista Matawalle wajen kara karfafa tsaron Nijeriya - Kungiyar Northern Concern Citizens
Ƙungiyar Northern Concerned Citizens ta yaba da irin namijin kokarin ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammad Matawalle, MON, wajen sauya tsarin tsaro da karfafa guiwar jami’an tsaro a fadin Nijeriya.
Sakataren ƙungiyar ‘yan Arewa masu kishin kasa, Muhammad Abdullahi, ya ce, tun bayan da aka nada Matawalle mukamin ministan tsaro a watan Agustan 2023, ya nuna ƙwazo, hangen nesa da jajircewa wajen tabbatar da ci-gaban da ake samu a yaki da ta’addanci da ‘yan bindiga.
Haka kuma, Dr Bello Matawalle ya nuna kwarewa a shugabanci mai tasiri wanda ya kara wa hukumomin tsaro kwarin guiwa, tare da bai wa ‘yan Nijeriya sabuwar fata da kwarin guiwa kan abubuwan da s**a shafi tsaro.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa yadda Matawalle ke tallafar haɗin-kai tsakanin hukumomin tsaro, tare da kira da a karfafa saka hannun jari da kuma samar da wadatattun kudade ga bangaren tsaro domin kara daukar matakai wadanda za su yi tasiri kan yaki da ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.
Abdullahi ya kara da cewa, kulawar ministan ga walwala da jin dadin sojoji, musamman ta hanyar shirye-shiryen inganta harkar lafiyar sojoji da haɗin guiwa da ƙasashen waje, na nuna irin shugabanci mai cike da kishin jama’a da Matawalle ke jagoranta.
A cewarsa, shugabancin Bello Matawalle ya bambanta domin ba kawai filin daga ya mayar da hankali ba, lafiyar ma’aikatansa ma bai manta da ita ba. Wannan shi ne ainihin shugabanci na gaskiya a bangaren tsaro.
A karshe, Abdullahi ya bukaci gwamnati, majalisa, kamfanoni da jama’a da su ci-gaba da mara wa ma’aikatar tsaro baya wajen tabbatar da ci-gaba, inganta kayan aiki da karfafa dabarun tsaro.
Abdullahi ya ce, “Ginin da Matawalle ke shimfidawa a yau shi ne ginshikin karfin tsaron Nijeriya na shekaru masu zuwa.”