05/06/2026
Hon. Kareema Abdullahi (Mai Dan Kwali) ta yi kira ga Jam'iyyar ADC da Hukumar INEC mai zaman kanta da su yi mata adalci dangane da zaben fidda gwani na kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da aka gudanar.
Ta bayyana cewa ba a gudanar da zaben cikin adalci da gaskiya ba, inda ta ce an tauye hakkinta kuma ba a yi mata adalci ba a yayin gudanar da tsarin zaben.
Kareema Abdullahi ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su duba korafinta tare da tabbatar da an yi wa kowane dan takara adalci domin kare martabar dimokuradiyya da amincewar al'umma.
Arewa Hub