29/07/2026
Gwamnatin Iraƙi ta bayyana cewa tana da cikakkiyar aniyar ƙarfafa zaman lafiya a cikin ƙasar da kuma ba da gudummawa wajen tabbatar da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.
A wata sanarwa da Ofishin Firaministan Iraƙi ya fitar, gwamnatin ta ce ba ta da niyyar shiga rikice-rikicen yankin, tare da yin kira ga dukkan ɓangarori da su guji ɗaukar matakan da za su ƙara ta'azzara rashin zaman lafiya.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa magance hare-hare da duk wasu batutuwan tsaro hakki ne na gwamnatin Iraƙi kaɗai, kuma hukumomin tsaro ne kawai ke da alhakin gudanar da irin waɗannan ayyuka.
Follow us now 👉 Sabo Pen