29/06/2024
Shawarwari 7 masu muhimmanci Wadda zasu kaika ga Nasarar a Trading 📈
0️⃣1️⃣ Idan kana rawan banjo a kasuwa, kayi gaba taku ɗaya, baya taku uku, to kuɗin da kake shiga dasu kasuwa ne babu daidaito - position sizing kenan, wani loakci ka sakawa coin $10 wani kuma ka saka masa $100.
Shawara: ka ayyana wani fix amount ga kowane trade komai kyawun set-up ɗinka.
0️⃣2️⃣ Idan kuma yawan asarar da kake yi a kasuwa sunfi ribarka, to akwai alamun kana tirsasa kanka shiga kasuwa koda kuwa babu set-up mai kyau
Shawara: Ka rika neman set up masu kyau, mai Risk to reward (RRR) 1:3 zuwa sama. Sannan ka zaɓi babban zangon lokaci kamar 4H wajen shiga kasuwa
0️⃣3️⃣ Idan ribar da kake samu ne yake kaɗan, akwai yiwuwar kana gaggawar fita daga kasuwa saboda gudun rasa ɗan ribar daka samu.
Shawara: Ka rika bin abinda chart ɗinka ya baka, ko Dubai ko Dawanau 😂. Ko take profit ko stoploss. Sannan ka rage zama akan screen da yawan duba wallet.
0️⃣4️⃣ Idan ka fuskantar manyan asara a kasuwa, ya kamata ka fara amfani da stoploss 🛑
0️⃣5️⃣ Idan ka tsinci kanka kana tsaye a wuri guda ka kasa yin gaba ko baya, ka gama duk analysis na duniya, amma baka iya shiga kasuwa, kana fama da decision paralysis.
Shawara: Ka rage yawan tools ɗinka na analysis, sannan ka fara trading ko da da $5. A hankali sai ka gina confidence ɗinka.
0️⃣6️⃣ Idan ka tsinci kanka kullum kana cikin USDT ka kasa sayan coins.
Shawara: kana iya fara P2P ko bunburutu a Bybit ko Bitget, ko ka sayi BTC, BNB da ETH ka rike.
0️⃣7️⃣ Idan wancan bullrun baka sami x5 ko sama da haka ba, to kana wasa da trading ɗinka, ya kamata ka rike shi hannu bibbiyu.
Ka rika analysis, ka rika research a Twitter, da sauran kafafe da ake samun bayanai masu inganci.
Idan ka nakalci waɗannan shawarwari 🧠 zaka rage kaso mai yawa na kurakurai da kake yi a kasuwa.
Kuma tabbas zaka sami nasara 🏆 a trading ɗinka.
Yana da kyau muyi printing 📜, sannan mu like wannan rubutun a wuraren da muke trading don muhimmancin ilimi dake ciki. ✍🏼
Mahmoud Muh'd Sardauna