Taskira Hausa

Taskira Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Taskira Hausa, Media/News Company, Police Station Road, Gwarinpa.

MANUFAR TASKIRA HAUSA

Taskira Hausa Jarida ce ta Yanar Gizo wacce ta zo da manufar samar da sahihan labarai da ingantattun rahotanni na ci gaban ƙasa da haɗin kai tare da bada gudun mowa

SHUGABA TINUBU YA JI KOKEN KUShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fito gaba haɗi domin share kukan al'ummar ƙasa musamman ...
31/07/2023

SHUGABA TINUBU YA JI KOKEN KU

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fito gaba haɗi domin share kukan al'ummar ƙasa musamman dangane da halin matsi da ake ciki.

A jawabin da ya gabatar ta kafafen yaɗa labarai a yammacin yau ya bayyana yadda gwamnati ta shirya antayo maƙudan kuɗaɗe ta fannoni da dama domin ragewa mutane raɗaɗin gyaran karayar tallafin mai da ake ciki a halin yanzu. Ga kaɗan daga cikin tanade-tanaden:
1. Bawa masu masana'antu 75 jari mai rangwame har na naira biliyan ɗaya kowannen su. Wanda za su biya a tsahon watanni 60.

2. Masu matsaƙaita da ƙananan sana'o'i za su amfana da naira biliyan 125 domin haɓɓaka jarinsu.

3. Daga cikin waccan biliyan 125 gwamnati za ta bada jari kyauta (mai haɗe da sharaɗi) na naira 50,000 ga masu ƙananan sana'o'i mutum 1,300 a kowace ƙaramar hukuma.

4. Sauran biliyan 75 za su tafi wajen masu matsaƙaitan sana'o'i inda za a bawa mutum 100,000 rance mai rangwame na naira 500,000 zuwa miliyan ɗaya wanda za su biya a hankali cikin shakara uku.

5. Tunda sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, Shugaban Ƙasa ya bada umarnin fito da abinci har ton 200,000 tare da takin zamani ton 225,000 domin rabawa ga mabuƙata da manoma.

5. Nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samar da ƙananan moticin bus masu amfani da gas har guda 3,000 domin kawo rangwame a kuɗin sufuri da jama'a ke fama da shi. Waɗannan motoci za a raba su ne ga kamfanonin sufuri domin gudanar da su.

6. Haka nan kuma gwamnati ta ware maƙudan kuɗaɗe domin noma hekta 500,000 a ɓanagarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana'a ta wucin-gadi.

A ƙarshe, ga waɗanda s**a saurari cikakaken jawabin za su ji yadda Shugaba Tinubu ya nuna tausayawa da halin da ake ciki, ya bada haƙuri, ya kuma sha alwashin ƙawo ƙarshen wannan yanayi cikin gaggawa da taimakon Allah.

©Abdulaziz Abdulaziz

Motar Dangote ta Afkawa wani gida ta halaka mutum 3 suna kwance a daki a Zariya.Motar dakon kaya na Dangote ta yi sanadi...
31/07/2023

Motar Dangote ta Afkawa wani gida ta halaka mutum 3 suna kwance a daki a Zariya.

Motar dakon kaya na Dangote ta yi sanadiyar halaka mutum 3 a Zariya.

Da sanyin safiyar yau na litini Jaridar ALFIJIR HAUSA ke samun labarin tabbacin cewa, mutum uku sun rigaye mu gidan gaskiya a sak**akon afka masu da motar Dangote ta yi har cikin ɗaki.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi cikin wani Anguwa da ake kira da anguwar juma dake birnin Zariya.

Wanda abin ya faru a idonsa ya ci gaba da shaidawa jaridar ALFIJIR HAUSA cewa, motar ta ƙwacewa direbanne a bayan haka sai ta Afka wani gida inda ta halaka mutum 3 suna kwance a cikin ɗakinsu.

Manyan laifukan da Bazoum ya yi wa faransa daya sa take ƙoƙarin ganin bayansa.1- Ya ki yarda kasar ta ci gaba da bautar ...
26/07/2023

Manyan laifukan da Bazoum ya yi wa faransa daya sa take ƙoƙarin ganin bayansa.

1- Ya ki yarda kasar ta ci gaba da bautar da kasarsa k**ar yadda ta saba.

2- Ya nu na a fili cewa yana son kasarsa ta daina amfani da Saifa domin samawa kasar kudi mallakinta.

3- Kwanakin baya wajen buɗe matatar Man Fetur ɗin Dangote a Legas, ya yi jawabi da Hausa mai makon Faransanci, hakan ya janyo manyan yan bokon kasar na Nijar suke ƙalubalnatansa na karya dokokin ƙasa.

4. Ya amince da canza taken kasar akan wanda faransa ta Samar masu tun wancan Lokacin.

Najeriya ta amince da ɓullo da sabbin matakai don sauƙaƙa rayuwaMajalisar kula da Tattalin Arziƙi a Najeriya ta sanar da...
20/07/2023

Najeriya ta amince da ɓullo da sabbin matakai don sauƙaƙa rayuwa

Majalisar kula da Tattalin Arziƙi a Najeriya ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta ɗauka don samar wa ‘yan ƙasar sauƙin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a ƙarshen taron wata-wata da ta yi a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima.

Taron na tsawon kimanin sa’a shida ya fi mayar da hankali a kan batutuwa guda biyu da s**a fi tasiri wajen jefa ‘yan ƙasar cikin mawuyacin hali. Wato janye tallafin mai da kuma karyewar darajar naira.

Bayan tafka muhawara da musayar yawu, taron ya amince da ɗaukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ‘yan Najeriya musamman mafi ya rauni daga cikin halin da s**a shiga. Daga ciki akwai buƙatar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sauƙi ko dai ta hanyar raba tallafin kuɗi ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka ma an amince da bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin kuɗi a kan albashinsu, tsawo wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma'aikata da ‘yan fansho dukkan bas**an da suke bi.

Waɗannan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar kuɗin da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin kuɗi.

Bugu da ƙari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya mak**ashin da ababen hawa s**a fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau'in iskar gas da ake kira CNG a taƙaice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.

Jihohin ƙasar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.

Amma duk waɗannan matakai, sai bayan an aiwatar da shirin raba kayan abinci ga ɗaukacin jihohin ƙasar domin sauko da farashinsa, a cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Majalisar dai ta ce tana sane da mawuyacin halin da ‘yan ƙasar ke ciki don haka ɗaukar waɗannan matakai sun zama wajibi domin kaucewa yanayin da wahala za ta tura ‘yan ƙasar bango har su yi bore.

Wani babban batu da ‘yan kasar ga alama suke son su ji matsayar majalisar a kai shi ne amincewa ko akasin haka da bukatar ƙarin albashi ga ma’aikata zuwa aƙalla N200,000 k**ar yadda ‘yan kwadago ke nema, sai dai ga alama babu wata matsaya da aka cimma a kan haka.

FITACCIYAR Jarumar Finafinan kannywood Hadiza Aliyu Gabon Ta Bayyana cewa kar fa jama'a su Dinga Tunanin Ta Rasa budurci...
12/07/2023

FITACCIYAR Jarumar Finafinan kannywood Hadiza Aliyu Gabon Ta Bayyana cewa kar fa jama'a su Dinga Tunanin Ta Rasa budurcinta.
Har yanzu Yana Nan Kuma Ta kame kanta
Kuma Sai ta Kai Abinta dakin mijinta

Jarumar ta Kara da cewa Shekaruna 28 Kuma har Yanzu ni Budurwa ce ban Taɓa Sanin Ɗa Namiji ba.

~ It'z Kamalancy

An k**a wata likita a Nijeriya da laifin sumbatar wani maras lafiya har na tsawon wasu sa'oi dake kwance a ranga-ranga b...
12/07/2023

An k**a wata likita a Nijeriya da laifin sumbatar wani maras lafiya har na tsawon wasu sa'oi dake kwance a ranga-ranga bisa gadon asibiti.

Musulmai a Pakistan sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai game da ƙona Al-Ƙur'ani a wajen wani masallaci da ke ƙasa...
10/07/2023

Musulmai a Pakistan sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai game da ƙona Al-Ƙur'ani a wajen wani masallaci da ke ƙasar Sweden.

Mutane da dama a duk faɗin duniya sun yi Allah-wadai da lamarin wanda ya janyo ce-ce ku-ce.

Shafaffe Da Mai A Garin Zaria Yashiga komar Jami'an TsaroDaga Sufiyanu SunusiBisa abinda yafaru a Unguwan Magajiya Zaria...
10/07/2023

Shafaffe Da Mai A Garin Zaria Yashiga komar Jami'an Tsaro

Daga Sufiyanu Sunusi

Bisa abinda yafaru a Unguwan Magajiya Zaria wanda Mai Saurata Marafan Yamman Zazzau ya tsawatar ma matashin Nan Sabo Yahaya bisa zargin sa da lalata Wani yaro wanda hakan yakawo Cece kuce musamman tsakanin sa da mutanen Unguwan Magajiya baya ga irin gudunmuwar da yake bayarwa musamman na Jagorantar 'yan sintiri da biyan su albashi da duk wata gudunmuwar irinsu biki da rashin lafiya da sauran su domin yaukaka zumunci a tsakanin su.

Bisa bincike da masana s**ayi yanuna cewa mafi yawan wadannan al'amura suna faruwa ne sak**akon rashin fahimta dake tsakanin basaraken Marafan Yamma Zazzau da wasu kalilan masu fada aji a Unguwan shiyasa suke tunzura wasu fusattatun matasa suna hayaniya a fili da Kuma kafar sada zumunta ta zamani(Social Media)

Zanso Mai karatu yakaranta wannan Takardan Koke dake hade da rubutun nan domin yatabbar da dalilin da yasa jiya lahadi 9 ga watan yuli 2023 jami'an tsaron acikin farin kaya s**a shigo cikin unguwan ta Magajiya s**a yi ram da wanda ake zargi wato Sabo Yahaya bisa dalilin da yasa mahaifin yaron (Aliyu Dan Asabe da ake zargin an lalata yakai karar sa offishin hukuma domin abi masa hakkin sa. Shiyasa k**a Aliyu Sabo da ake zargi bashida alaka da Marafan Yamman Zazzau, shi uban yaro ne yasa aka k**asa domin a binciki wanda ake zargi.

Bisa abin mamaki Kuma, sai ga Wanda ake zargi da cewa anyi masa dan Karen duka jiya Yana cikin unguwa Yana yawo lafiyan sa lau jami'an tsaro s**a k**asa Domin Zurfafa bincike da Kuma tabbatar da adalci

Son Rai Shi ke kawo Bacin Rai!!!

TARBIYYA DA AL'ADAN JAGORORIN AL'UMMA A KASAR HAUSAA shekarun da s**a shud'e da yawan masu rike da sarautun gargajiya k*...
08/07/2023

TARBIYYA DA AL'ADAN JAGORORIN AL'UMMA A KASAR HAUSA

A shekarun da s**a shud'e da yawan masu rike da sarautun gargajiya k**a daga Mai Unguwa, Dakace, Malamai, Shuwagabannin Matasa, Hakimai, har zuwa Sarki da sauran su, sune keda hakkin kula da tarbiyan jama'an su bayan iyaye a cikin gida.

Shiyasa ma a wancan Lokacin zaka ga Sarki shine Limamin Gari, Alkali, Jami'in tsaro da Sauran su.

Duk matashi ko yaro A cikin Unguwa daya daga cikin Jagororin da na lissafa suna Iya hukunci akan matasa da yara a cikin Unguwa ko dan Waye saboda gyaran tarbiya, da fadin "bahaushe da yace gyara kayan ka bazai zamto sauke mu raba ba".

A duk Lokacin da akace matasa zasuyi abinda s**a so a unguwa Kuma Babu Mai tsawata masu to gaskiya sai abinda s**ayi, saboda kafin ace aje gurin hukuma abu ya lalace.

Yanzu a misali sai ace a cikin Unguwa kuga Wani Yana bata maku yaro da neman sa ta baya, sai ku ki hukunci a kansa Saboda daukan doka a hannu babu kyau? Ko yaro acikin gidan ku yana rashin tarbiya sai a zura masa ido ko a tsaya jiran hukuma har tazo ta gyara tarbiyan sa?

Misalin irin abinda yafaru kenan a Zaria da dakataccen basarake Marafan Yamman Zazzau da Wani matashi wanda yake zargi yana bata wani a cikin wani kango, Wanda a matsayin sa na Mai saurauta a Masarautar Zazzau Kuma wakilin al'ummar Unguwan Magajiya dake Zaria yayi amfani da damar sa na jagora ya hukunta sa daidai gwargwado saboda hakki na makota ka da hakkin tarbiyan matasan yankinsa a Wanda yarataya a hannun su.

Bayan hukunci da dakataccen Basarake Marafan Yamman Zazzau yayi akan matashin da ake zargi da lalata yaran mutane a unguwa Hakan yasa wasu maras kishin al'umma sun shiga media sunata bata masa suna, Wanda mu a yankin mu ta kasar hausa musamman a Yanzu munada bukatan irin wadannan mutane. Saboda duk Wanda yake bin wasu ta baya Shima ana binsa Kuma Suma yaran da yabi zasu bi wani kaga daga nan duk Al'umma zata gurbace da tarbiya irin ta zamanin al'umman Annabi Lud'

Kuma harda wasu manya sune da shiga gidan Radio suna bata Alh. Mustapha Adamu Ubaidu dakataccen (Marafan Yamman Zazzau) akan wannan lamari, Kuma mu Muna ma da tambaya wai shin meye ke tsakanin wadannan mutanen da suke fita Radio da wannan matashi da ake zargi da bin Maza? Sannan Suma sauran masu ruwa da tsaki da s**a ruwa s**ayi Tsaki, meye nasu aciki.?

Sannan har ila yau shifa Mai Girma dakataccen Marafan Yamman Zazzau dinnan shine Jagoran 'yan sintiri na tsaron yankin su, Wanda kullun basa bacci Domin bada kariya ta tsaro ga yankin Unguwan su ta Magajiya a irin kokarin nasa yasa aka dauki 'yan sintiri da duk wata shi ke biyan su albashi, so a wannan yanayin ne fa yaga Wani na aikata ba daidai ba yayi hukun ci a Iya matsayin sa na Jagoran al'umma a unguwa sai wasu s**a fake da haka saboda Wani abu daban dayake a ransu na hassada.

Mufa mutanen Zaria wayayyu ne, bamu kin namu don ayabemu kuma waya tabamin dana in tabi nasa baya cikin al'adun mu.

Muna kira na gagggawa Domin yima masarautar Zazzau da basaraken ta adalci.

Ahmed Tijjani
Media Consultant,
Marubuci, Danjarida, Mai kishin Masarautar Zazzau.

YANZU-YANZU: An Garzaya D Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari Asibiti Sak**akon Karaya Da Ta Samu A KafaMAJIYA: Daily ...
20/11/2022

YANZU-YANZU: An Garzaya D Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari Asibiti Sak**akon Karaya Da Ta Samu A Kafa

MAJIYA: Daily Nigerian

Ƴan Sanda a garin zariya sun k**a wani matashi mai suna Ali boss Ɗan tudun Wada da laifin lakaɗawa mahaifiyarsa dukan ts...
19/11/2022

Ƴan Sanda a garin zariya sun k**a wani matashi mai suna Ali boss Ɗan tudun Wada da laifin lakaɗawa mahaifiyarsa dukan tsiya.

Address

Police Station Road
Gwarinpa

Telephone

+2347087896090

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskira Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share