Karamchi

Karamchi Gudan Labarai

Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon...
27/08/2026

Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa.

Kungiyar ta ce korafinta ya ta’allaka ne musamman kan nada Sheriff a matsayin mai kula da yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa maso Gabas, a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben 2027.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Ahmad Zangina, ya ce kungiyar na nan daram kan kudirinta na ganin an sake zaben Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gangamin neman masa goyon baya ga talakawa ba muddin wannan tsari bai sauya ba.

DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawow...
26/08/2026

DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawowa gida Najeriya.

‎Dubban magoya baya sun fito domin tarbar Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, bayan dawowarsa gida Najeriya, lamarin da ya sake jawo zazzafar muhawara kan ƙarfin siyasar Matawalle da kuma yiwuwar samun gagarumin goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

‎Hotuna da bidiyoyin taron sun nuna yadda magoya baya s**a fito cikin ɗimbin jama'a domin tarbar tsohon gwamnan jihar Zamfara. Wannan gagarumar tarba ta sa wasu masu sharhi da magoya bayan jam'iyyar APC ke cewa alkawarin tattara kuri'u miliyan 20 daga Arewa domin Tinubu na iya zama abin da za a iya cimmawa, idan aka yi la'akari da irin ƙarfin da manyan jiga-jigan siyasar Arewa ke da shi a matakin ƙasa da ƙasa.

‎A kwanakin baya, wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu mai suna Northern Vanguard for Asiwaju ta bayyana aniyarta ta taimaka wajen tattara akalla kuri'u miliyan 20 ga shugaban ƙasar a zaɓen 2027, tana mai bayyana cewa za ta dogara da tsarin siyasa da magoya bayan Matawalle da sauran jiga-jigan APC a fadin Arewa.

‎Amma babbar tambayar da mutane ke yi ita ce: Shin taron dubban mutane domin tarbar Matawalle yana nufin za a iya sauya wannan taro zuwa kuri'u miliyan 20?

‎Amsar ita ce, yana yiwuwa a siyasance, amma ba abu ne mai sauƙi ba.

‎Tarbar jama'a na iya nuna farin jini, tasiri da ƙarfin tsarin siyasa, amma zaɓe yana buƙatar abubuwa da dama. Dole ne a tabbatar da rajistar masu zaɓe, fitowarsu ranar zaɓe, haɗin kai tsakanin manyan jiga-jigan siyasa, da kuma yadda jama'a ke kallon manufofi da ayyukan gwamnati.

‎Matawalle dai ya sha bayyana cewa yana da yakinin Arewa za ta nuna goyon bayanta ga Tinubu a 2027, yana mai cewa ayyukan gwamnati a yankin za su iya ƙara wa shugaban ƙasar farin jini.

DA ƊUMI-ƊUMI: Dara Ta Ci Gida — An Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina Kan Zargin Lalata Allunan SiyasaRahotanni sun bay...
25/08/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Dara Ta Ci Gida — An Tsare ADC da CSO na Gwamnan Katsina Kan Zargin Lalata Allunan Siyasa

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro biyu da ke kula da tsaron Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wato Aide-de-Camp (ADC), Hassan Bello, da Chief Security Officer (CSO), suna tsare a hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ke Abuja tun ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an tsaron biyu suna hannun jami’an tsaro a Abuja, yayin da aka ce Chief of Staff na Gwamnan Katsina, Alhaji Abdulkadir Nasir, ya je Abuja domin neman a sake su, amma ƙoƙarinsa bai yi nasara ba, k**ar yadda jaridar Katsina Times ta rawaito.

Haka kuma, wata majiya ta ce Gwamna Dikko Radda da kansa ya yi ƙoƙarin ganin an saki jami’an tsaron nasa, sai dai har zuwa yanzu ba a samu nasarar sakin su ba.

An ce an tsare jami’an ne sak**akon zargin hannu a lalata wasu manyan allunan talla da ke kan hanyar daga Modoji Roundabout zuwa Gidan Gwamnatin Katsina.

Wasu daga cikin allunan na ɗauke da hotunan Gwamna Radda, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da wasu fitattun ’yan siyasa.

Rahotanni sun ce an lalata wasu daga cikin allunan, musamman waɗanda ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabir Masari.

Bayan faruwar lamarin, an kai ƙorafi ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar DSS, lamarin da ya sa hukumomin tsaro s**a fara gudanar da bincike.

A yayin binciken, an k**a wani mutum da ake zargin jagoran wata ƙungiyar siyasa ne a Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Aminu Nasta.

Majiyoyi sun ce bayan k**a Aminu Nasta da kuma bayanan da aka samu yayin bincikensa, jami’an tsaro sun gayyaci ADC da CSO na Gwamna Radda domin yi musu tambayoyi.

Ana zargin jami’an tsaron biyu da kasancewa suna da masaniya kan lamarin, ko kuma sun taimaka wajen kare wasu daga cikin mutanen da ake zargi da lalata allunan da ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da Ibrahim Masari.

Sai dai, har yanzu ba a bayyana wata hujja a bainar jama’a da ke tabbatar da cewa jami’an biyu sun hannu kai tsaye wajen lalata allunan ba.

Lamarin ya sake jawo hankali kan rikicin siyasa da ake zargin yana ƙara tsananta tsakanin wasu ɓangarori a cikin jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, musamman tsakanin masu goyon bayan Gwamna Radda da ɓangaren da ake dangantawa da Ibrahim Masari da wasu manyan ’yan siyasa a Abuja.

Wasu ’yan siyasa na ganin cewa rikicin cikin gida na APC a Katsina na iya ƙara ɗaukar sabon salo yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, musamman idan aka fara amfani da hukumomin tsaro wajen magance rikicin siyasa.

Har yanzu dai akwai tambayoyi kan dalilin da ya sa aka tsare jami’an tsaron da ke kula da lafiyar Gwamnan Katsina, da kuma ko akwai wata hujja da ta tabbatar da alaƙarsu da lalata allunan kamfen.

Ana kuma kira ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su bayyana dalilin tsare ADC da CSO, tsawon lokacin da za a ci gaba da tsare su, da kuma irin laifin da ake bincikensu a kai.

Ci gaba da tsare jami’an biyu ya ƙara haifar da tambayoyi kan yadda rikicin siyasar APC a Katsina ke ƙara shiga cikin harkokin tsaro da gwamnatin jihar, yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Fitaccen ɗan siyasar nan kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya sha alwashin magance matsalar r...
23/08/2026

Fitaccen ɗan siyasar nan kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya idan ya yi nasara a zaɓen 2027.

Donald Duke ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya yi bayani kan matakan da zai ɗauka wajen magance rashin tsaro da kuma wasu matsalolin da s**a shafi ci gaban Arewacin Najeriya.

Ya bayyana talauci a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da s**a taimaka wajen taɓarɓarewar tsaro a Arewa, yana mai cewa matsalar ba za ta warware ta hanyar matakan tsaro kaɗai ba, sai an inganta tattalin arziki da samar wa jama’a hanyoyin dogaro da kai.

Duke ya ce gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar zamani wajen kula da iyakokin Najeriya, ciki har da amfani da jirage marasa matuƙa da tauraron ɗan Adam domin gano masu shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba da kuma bai wa jami’an tsaro damar ɗaukar mataki cikin sauri.

Ya ce duk da cewa akwai masu aikata laifuka da ke shigowa Najeriya daga wasu ƙasashe, yawancin matsalar ’yan bindiga ta samo asali ne daga cikin gida, don haka akwai buƙatar magance matsalolin cikin gida maimakon ɗora alhakin rashin tsaron gaba ɗaya kan baƙi.

A ɓangaren noma, Duke ya ce akwai madatsun ruwa tsakanin 300 zuwa 400, musamman a Arewacin Najeriya, waɗanda za a iya amfani da su wajen bunƙasa noman rani da samar da abinci a duk shekara idan aka farfaɗo da su tare da amfani da su yadda ya k**ata.

Ya kuma bayyana ma’adanai a matsayin wani muhimmin ɓangare na arzikin Arewa bayan noma, yana mai cewa akwai buƙatar tantance adadin ma’adanai da ake da su a jihohi domin samar da sahihan bayanan da za su jawo hankalin masu zuba jari.

Duke ya ce za a tsara harkar haƙar ma’adanai domin tabbatar da cewa al’ummomin da ake hako albarkatun a yankunansu, ƙananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya suna cin gajiyar su, tare da hana masu aikata laifuka amfani da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.

Kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, Duke ya ce ilimi ya k**ata ya zama wajibi kuma kyauta, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ilimi da wata sana’a da za ta ba shi damar dogaro da kansa.

Ya kuma yi magana kan matsalar shan miyagun ƙwayoyi a Arewa, inda ya danganta yaɗuwarta da rashin aikin yi, takaici da rashin kyakkyawar makoma ga matasa, tare da cewa samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a na daga cikin hanyoyin rage matsalar.

Duke ya ce babban burinsa shi ne a mayar da kowace jiha cibiyar tattalin arziki, ba cibiyar gudanar da siyasa kawai ba, ta yadda jama’a za su samu damar aiki da bunƙasa rayuwarsu a jihohinsu ba tare da tilasta musu ƙaura zuwa Abuja, Lagos ko wasu manyan birane ba.

Ya kuma bayar da shawarar samar da wutar lantarki a matakin yankuna, inda ya ce samar da cibiyoyin mak**ashi a yankunan Sanatoci zai taimaka wajen kusantar da samar da wutar lantarki ga jama’a da bunƙasa tattalin arzikin yankunan ƙasar.

TIRKASHI: Shekarun Rayuwarmu Ba Mu Taba Ganin Jami’in Gwamnati Ya Zo Kauyenmu Don Samar da Makaranta, Asibiti Ko Wutar L...
15/08/2026

TIRKASHI: Shekarun Rayuwarmu Ba Mu Taba Ganin Jami’in Gwamnati Ya Zo Kauyenmu Don Samar da Makaranta, Asibiti Ko Wutar Lantarki Ba — Mazauna Kauyen Boje, Daura

Wani dattijo mai suna Usman Dauda, ɗan asalin Kauyen Boje da ke Daura, Jihar Katsina, ya bayyana cewa ya shafe shekaru 75 a duniya, amma bai taba ganin wani jami’in gwamnati ya zo kauyen nasu da nufin samar da makaranta, asibiti ko wutar lantarki ba.

Usman Dauda ya ce tun tasowarsa yana da burin yin karatun zamani da na addini, sai dai rashin makaranta a kauyen Boje ya hana shi samun damar cimma wannan buri.

Ya bayyana cewa matsalar rashin makaranta ta dade tana addabar al’ummar yankin, musamman yara da matasa, wadanda ke fuskantar matsaloli wajen samun ilimi.

A nasa bangaren, wani mazaunin kauyen mai suna Ibrahim Iliyasu, ya bayyana cewa akwai tazarar kusan kilomita 20 tsakanin Kauyen Boje da makarantar da ta fi kusa da su.

A cewarsa, wannan nisa ya sa yara da dama ba sa iya zuwa makaranta, lamarin da ke haifar da karuwar yawan mutanen da ke tasowa ba tare da samun cikakken ilimin zamani ko na addini ba.

Mazauna Kauyen Boje sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da suke ciki, inda s**a yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da Gwamnatin Tarayya da su duba matsalolin da suke fuskanta tare da gina makaranta a yankin, da kuma samar da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

Sai dai a nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Daura, Bala Musa Daura, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina na kokarin bunkasa harkar ilimi a fadin jihar.

Bala Musa Daura ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa harkar ilimi, ciki har da samar da kujeru da gyaran makarantu a Daura da sauran sassan jihar.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da daukar matakan inganta harkar ilimi tare da samar da abubuwan more rayuwa a makarantu, domin tabbatar da cewa yara da ke yankunan karkara sun samu damar samun ilimi k**ar sauran al’ummar jihar.

‎Ana Zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo da K**a Wani Matashi Saboda Bayyana Ra’ayinsa na Siyasa‎Ana zargin Shugaban Ka...
11/08/2026

‎Ana Zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo da K**a Wani Matashi Saboda Bayyana Ra’ayinsa na Siyasa

Ana zargin Shugaban Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano, Hon. Lawan Najume Kabo, da hannu wajen k**a da tsare wani matashi mai suna Aliyu Muhammad Haruna, wanda aka fi sani da Babagana, bisa zargin ya bayyana ra’ayinsa kan wasu batutuwan siyasa.

An bayyana hakan ne cikin wata takardar ƙorafi mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Agusta, 2026, wadda aka miƙa wa Sufeto-Janar na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya a Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Louis Edet House, Abuja.

Takardar ta ƙunshi ƙorafi kan k**awa da tsarewa ba bisa ka’idar doka ba, da kuma zargin amfani da ikon ’yan sanda ba daidai ba wajen k**a matashin.
‎A cikin ƙorafin, lauyoyin Aliyu Muhammad Haruna sun bayyana cewa:

“Mu ne lauyoyin Mr. Aliyu Muhammad Haruna (Babagana), kuma bisa umarninsa, mun rubuto wannan wasiƙa domin sanar da ku halin da ya dabaibaye k**awa da tsare shi da jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kabo.”

A cewar takardar, lauyoyin sun yi zargin cewa k**awa da tsare Babagana ya faru ne bisa umarni ko sa hannun Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo.

‎LauyoyinLauyoyin sun kuma nemi a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano halaccin k**awa da tsarewar, yanayin da ya kai ga jami’an ’yan sanda ɗaukar matakin, da kuma rawar da Shugaban Karamar Hukumar ya taka a cikin lamarin.

Takardar ta bayyana Babagana a matsayin ɗan Najeriya, ɗalibi kuma ɗan asalin Jihar Kano, tare da cewa, bisa bayanan lauyoyinsa, ba shi da wani tarihin aikata laifi da ya shafi wannan ƙorafi.


A ranar 3 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kabo sun je gidan Babagana da ke Gidan Alh. Haruna, Kabo, inda s**a k**a shi tare da kai shi ofishin ’yan sanda.

A cewar Babagana, jami’an sun ɗauki matakin ne bisa umarni ko sa hannun Hon. Lawan Najume Kabo, Shugaban Karamar Hukumar Kabo.

Takardar ta ƙara da cewa Babagana ya taɓa samun rashin jituwa da Shugaban Karamar Hukumar kan wasu batutuwan siyasa da kuma yadda ake gudanar da harkokin ƙaramar hukumar.

Kafin k**a shi, Babagana ya kasance yana bayyana ra’ayoyinsa da rashin amincewarsa da wasu manufofi ko matakan gudanarwa da s**a shafi Shugaban Karamar Hukumar.

‎A halin yanzu, lauyoyin matashin suna neman a gudanar da bincike domin tabbatar da ainihin dalilin k**awa da tsare shi, da kuma gano ko an yi amfani da ikon ’yan sanda ba bisa ka’ida ba.

"Yanzu Na Dawo Gidan Mutunci Na Fita Daga Duhu Na Dawo Haske Cewar Dr. Aslam Aliyu Bayan Ta Gana Da Shugaba Tinubu" A wa...
03/08/2026

"Yanzu Na Dawo Gidan Mutunci Na Fita Daga Duhu Na Dawo Haske Cewar Dr. Aslam Aliyu Bayan Ta Gana Da Shugaba Tinubu"

A wani sabon salo da ya ɗauki hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya, tsohuwar ƙawanyar siyasar Atiku Abubakar, Dr. Aslam Aliyu, ta kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ziyara jim kaɗan bayan komawarta jam'iyyar APC, lamarin da ya ƙara jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.

Dr. Aslam Aliyu, wadda ta kasance cikin masu fafutukar siyasar Atiku Abubakar a baya, ta bayyana cewa ta yanke shawarar barin tafiyar adawa ne bayan ta gamsu cewa ba ta ga ingantaccen tsari ko sahihin shirin ceto Najeriya daga ɓangaren da ta fito ba. Ta ce ta zaɓi shiga APC ne domin bayar da gudummawa ga abin da ta yi imanin zai amfani ƙasa.

Masu goyon bayanta na bayyana matakin nata a matsayin "barin duhun siyasar adawa zuwa hasken tafiyar Bola Ahmed Tinubu," suna masu cewa ziyarar da ta kai wa Shugaban Ƙasa alama ce ta cikakken goyon baya ga manufofin gwamnatin APC da shirin Renewed Hope. Sai dai wannan furuci yana nuna ra'ayin magoya bayanta ne, ba tabbatacciyar gaskiya ba.

Masu nazarin siyasa na ganin sauya sheƙar Dr. Aslam Aliyu na iya ƙara ƙarfafa APC musamman a Arewacin Najeriya, duba da irin rawar da ta taka a siyasar adawa a shekarun baya. A nata ɓangaren, ta yi kira ga matasa, mata da sauran 'yan Najeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai domin tallafa wa shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

TIRKASHI: Lalle Dole mu ɗauki Ci gaban Al"umma Ya Zama a matakim Farko A Tsarin Mulki - Fahad Dankabo Jigo a jam'iyyar A...
20/07/2026

TIRKASHI: Lalle Dole mu ɗauki Ci gaban Al"umma Ya Zama a matakim Farko A Tsarin Mulki - Fahad Dankabo

Jigo a jam'iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Kabo, Fahad Muhammadu Adamu Dankabo, ya yi kira ga shugabanni da matasa da su fifita ci gaban al'umma da samar da ayyukan raya ƙasa masu ɗorewa fiye da anfani na siyasa.

A cikin wata doguwar sanarwa da ya fitar, a Shafinsa na Facebook, Fahad ya bayyana cewa duk da biyayyarsu ga tsarin jam'iyyar APC daga matakin ƙaramar hukuma har zuwa gwamnatin tarayya, ya k**ata shugabanni su sanya ci gaban al'umma a gaba, yana mai cewa an kafa siyasa ne domin bauta wa jama'a.

Ya kuma yi tsokaci kan ce-ce-ku-cen da s**a biyo bayan kalaman da ake Zargin Fahad Dankabo ne Yayi ko Fahad Shehu kan yadda ake tafiyar da harkokin Ƙaramar Hukumar Kabo. A cewarsa, "koma waye ne a tsakanin mu to sai me..? abin da ya fi muhimmanci shi ne a binciki gaskiyar zarge-zargen da ake yi maimakon mayar da hankali kan wanda ya furta su. Ya ƙara da cewa duk mai shakka kan halin da ake ciki zai iya ziyartar Kabo domin gani da idonsa.

Fahad ya yi kira ga matasa da kada su bari anfani na ɗan lokaci ya sa su sadaukar da makomarsu. Ya buƙace su da su haɗa kai cikin lumana wajen neman ingantaccen shugabanci da ci gaba, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Haka kuma, ya bayyana cewa yana da kyakkyawan zato kan manufar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen samar da ci gaba mai ɗorewa ta hanyar bunƙasa tattalin arziki da samar da yanayin da zai taimaka wa jama'a su dogara da kansu. Sai dai ya ce nasarar hakan na buƙatar haɗin kan al'umma da matasa wajen wayar da kan jama'a da kuma mara wa manufofin ci gaba baya.

A ƙarshe, Fahad ya jaddada cewa shugabanci amanar al'umma ne kuma jarabawa ce daga Allah, yana mai kira ga jama'a su tsaya a gefen gaskiya da ci gaba. Ya kuma kawo hadisin Annabi Muhammad (SAW) da ke umartar Musulmi su yi ƙoƙarin gyara abin da ba daidai ba gwargwadon ikon da Allah Ya ba su.

Sanarwar ta ƙare da neman afuwar duk wanda kalamansa s**a ɓata wa rai, yana mai cewa manufarsu ita ce ganin an samu ci gaba mai ɗorewa da zai amfani al'ummar Kabo baki ɗaya.

APC KABO:  Akwai Matsala" – Al'ummar Kabo Ba Zamu Yi APC Ba, Matukar Ba A Gyara Ba.Kungiyar Dalibai ta Kabo Local Govern...
16/07/2026

APC KABO: Akwai Matsala" – Al'ummar Kabo Ba Zamu Yi APC Ba, Matukar Ba A Gyara Ba.

Kungiyar Dalibai ta Kabo Local Government Students Association (KALSA) Tace Akwai bukatar gyara a fannin Ilimi a Karamar Hukumar Kabo Saboda haka Gwamnan Jahar kano yasa a gudanar da bincike mai zurfi kan Yadda Hon Lawan Najume Kabo Ke kashe kudin gwamnati a Kabo.

Comrade Malam Sani Kabo na daya Daga Cikin shugabanni kungiyar yace tun daga shekarar 2023 suke fafutukar nemo tallafi ga ɗaliban Kabo da ke karatu a manyan makarantu, musamman marayu da kuma 'ya'yan marasa ƙarfi, domin su samu damar ci gaba da karatunsu.

A Karshe sun yi kira ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dau matakin da ya dace Idan ba haka ba, tabbas akwai matsala a zabe mai zuwa.

16/07/2026

Barkan Mu Da Yamma Yanzu Haka Daga Ina Kuke Bibiyar Mu..?

Address

Gwarinpa

Telephone

+2348187689638

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karamchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category