20/05/2026
Mai neman jam’iyyar ADC ta tsayar da shi takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Niger mai wakiltar mazaɓar Kwantagora 1, Hon. Hamza Abdullahi, ya nemi goyon bayan ƴaƴan jam’iyyar tare da al’ummar mazaɓar domin samun nasarar tsayawa takara da kuma kai jam’iyyar ga cin nasara a zaɓe mai zuwa.
Hon. Hamza Abdullahi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aikowa TTN Hausa, inda ya ce yana da cikakken ƙuduri da shirye-shiryen yi wa al’ummar Kwantagora 1 hidima ta gaskiya idan har jam’iyyar ta amince da shi a matsayin ɗan takara.
Ya ce babban burinsa shi ne ganin an samar da wakilci nagari wanda zai kare muradun matasa, mata da sauran al’ummar mazaɓar a Majalisar Dokokin Jihar Niger.
A cewarsa, lokaci ya yi da za a bai wa mutane shugabanci mai cike da gaskiya da riƙon amana domin kawo ci gaba mai ɗorewa ga yankin.
“Na fito ne domin yi wa al’ummata hidima ba tare da son rai ko nuna bambanci ba. Ina mai tabbatar wa da ƴan jam’iyyar ADC da mutanen Kwantagora 1 cewa ba zan ba su kunya ba idan aka ba ni dama,” in ji shi.
Hon. Hamza ya kuma yi alƙawarin cewa zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar ADC tare da neman amincewar al’ummar mazaɓar domin jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a dukkan matakan zaɓe.
Ya ƙara da cewa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da siyasa cikin lumana, haɗin kai da mutunta juna.
Ɗan takarar ya kuma buƙaci magoya bayan jam’iyyar da matasa da su ci gaba da ba shi haɗin kai da addu’o’i domin cimma burin da aka sanya a gaba.
Ya ce nasarar ADC a Kwantagora 1 za ta zama wata sabuwar kafa ta ci gaba da inganta rayuwar al’umma a yankin.
A ƙarshe, Hon. Hamza Abdullahi ya jaddada cewa idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali wajen kawo ayyukan ci gaba, inganta walwalar jama’a da kuma tabbatar da cewa muryar mutanen Kwantagora 1 ta samu wakilci nagari a Majalisar Dokokin Jihar Niger.