
25/07/2025
IRÀN TA KADDAMAR DA TAURARON DAN ADAM NAHID-2....
Tauraron dan adam da Iran ta kera da kanta Nahid-2, an harba shi daga kasar Rasha a cikin kumbun Soyuz 2.1B zuwa sararin samaniya, wanda hakan ya zama babbar nasara ce ga ci gaban fasahar sadarwa ga kasar Iran.
An ƙera Nahid-2 domin habbaka sadarwa da fasahar zamani, zai kasance a sarari na tsawon shekaru 5 yana taimakawa Iran wajen tattara bayanan da Iran zata yi amfani dasu wajen sadarwa da tsaro..