04/01/2025
Ga cikakken bayani akan dokar 1:1!!!
Mutane da yawa suna tambayar menene dokar 1:1 wadda take addabar wasu kungiyoyi a manyan Lig-Lig daban-daban a fadin duniya musamman ma Barcelona a gasar La Liga.
Fagen Wasanni tayi muku bincike domin fitar daku daga duhu akan dokar 1:1 ta gasar La Liga!
Dokar 1:1 a gasar La Liga na nufin kayyade tattalin arziki wadda zata baiwa kungiya dama ta kashe adadin wasu kudade domin daukar sababbin yan wasa daidai da adadin kudin da ta samu wajen siyar da wasu yan wasan da kuma kudaden shigar ta.
Misali: Gaba daya asusun Bankin Barcelona 1000 ne a ciki, kuma wannan dubu dayar da ita suke baiwa yan wasa albashi da sauran dukkan wasu ayyukan kungiyar. Duk abun da Barcelona zata yi ba zai wuce na dubu daya ba. Kungiyar bazata iya kashe ko da Naira 100 ba akan dubu dayar nan domin ana so komai ya daidaita da abun da take samu da kuma abun da zata iya kashewa.
A lissafi idan kudin shigowar Barcelona dana siyar da yan wasanta 1000 ne to kungiyar bazata iya yin abun da ya wuce na 1000 ba domin a samu daidaito.
Kamar kan batun Dani Olmo da Pau Victor, an kayyadewa Barcelona iya adadin kudi da kuma abun da zata iya kashewa a kasuwa naira 1000 amma da kungiyar ta tashi sai ta kashe 1500, kuma gashi a bayyane kudinta 1000 ne, to a dokar La Liga dole sai ta san yadda akai ta samo cikon 500 din nan kafin a bata dama tayi Rijistar Olmo ko Pau Victor.
Hakanne yasa kungiyar ta saida kujerun VIP din ta domin ta daidaita kudadenta su koma 1500, Kuma kamar yadda rahotanni s**a bayyana sun samu damar yin hakan.
A takaice idan har aka ce kungiya ba ta kan dokar 1:1 to ana nufin basa kashe adadin kudin da suke samu, suna kashe fiye da abun da suke samu. Doka kuma tana so kungiya ta dinga kashe adadin kudin da take samu kar ta wuce sama da haka.
Idan baku manta ba a gasar Premier League an taba zarewa Everton maki saboda ana zarginsu da karya dokar kayyade tattalin arziki, FA na tuhumar Everton da kashe abun da yafi karfin tattalin arzikinsu hakanne y