05/02/2025
Mauludin Gwarazan Karbala: JAGORA YA GANA DA ‘YAN MU’ASSASATU ABUL FADL ABBAS (AS)
Daga Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake ganawa da mambobin Mu’assasatu Abul Fadl Abbas, wanda s**a hada har da bangarorinta irin su Kasshafa, Intizar da JASAZ, a ranar Talata 5 ga watan Sha’aban 1446 (4/2/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada bukatar sadaukarwa ga addini saboda Allah.
Jagoran, ya fara jawabinsa ne da taya ‘yan uwa murna da zagayowar kwanukan haihuwan gwarazan Karbala, wanda yace, ba zai zama a bisa hadari ba ne haihuwarsu ya zo a jere. “Na farkonsu Abi Abdullahil Husain (AS) wanda aka haifa ranar 3 ga watan Sha’aban; Sai kuma na biyunsu, dan uwansa wanda ya ba da ransa wajen kare shi, Abul Fadl Abbas, haihuwarsa ta kasance ranar 4 ga wata. Sai kuma Imam Zainul Abidin, wanda muna iya cewa shi ma ya fi kowa shan wahalar Karbala, don akan idonsa aka yi komai, shi kuma haihuwarsa ta zo ranar 5 ga wata.”
Yace: “Duk wadannan gwaraza, duk cikansu ‘rumuz’ (alamomi) ne na sadaukarwa, kowannensu an haife shi a gwagwarmaya, ya bar duniya a gwagwarmaya.”
Jagora ya bayyana yadda mahaifiyar Sayyid Abbas ta yi masa tare da ‘yan uwansa tarbiyar girmama ‘ya’yan Sayyida Zahra (SA), wanda haka yasa ko da suke uba daya, amma basu ganin ‘ya’yan Sayyida Fatima a matsayin ‘yan uwansu, face a matsayin shugabanninsu.
Yace: “Sayyida Ummul Banin, mahaifiyar Sayyid Abbas bata taba daukan Sayyida Zahra a matsayin kishiyarta ba, tana ganinta a matsayin shugabarta ne, kuma tace ma danta Abul Fadl Abbas, na haneka, kar ka kuskura kace ma Husaini ‘akhiy’ (dan uwana), kace masa ‘Sayyidiy wa maulaya’, domin Sayyidinka ne kuma Maulanka, shi shugabanka ne.”
Ya cigaba da cewa: “Saboda haka kullum shi Abul Fadl Abbas abin da yake kiran Imam Husaini shi ne ‘Sayyidi wa Maulaya’, sai sau daya rak ya taba kiransa da ‘dan uwansa, shi ne ranar Shahadarsa bayan an harbe shi da kibiya a wajen debo ruwa.”
Aduba comment