
02/07/2025
Bari muyi musu adalci dukkanin su
A zahirin Gaskiya tabbas Kannywood ta taimaki Alhikima domin dalilin ta aka sanshi ga bunƙasar kasuwanci dama samun cigaba da alfarma da yake dashi, wanda bai samu ba saida ya fara sanya tallan sa a Fina Finai.
Ta bangare guda kuma shima ya taimaki Kannywood domin shi ya fara bada tallan maganin sa da gaske, saida ya zama yana bada tallan sa a manya fina finan Kannywood, wanda ke samar musu da kudaden shiga.
Shi ya buɗe wa Kannywood kasuwa na karɓar talluka, musamman daga masu magunguna, inda masu magunguna s**a bazo Kannywood domin suma su tallata hajar su, duba da sun lura lallai hakan yana da anfani domin sun gani a tare da Alhikima.
Wanda hakan ya samarwa da masu shirya finafinan maƙudan kuɗaɗe koma ince suke samu, wanda har wasu masu shirin ke bugar ƙirjin cewa tun a talla da ake basu suke maida kudin film, kai akwai finafinan ma da in babu talla kudin su bazai dawo har su maida riba ba.
Tabbas Kannywood ta taimaki Alhikima shima kuma ya taimake ta.
Amma mu jama'ar gari bai taimake mu ba, kuma bai duba mana ba, domin shi ya buɗe kofar Tallan Maganin Istimna'i da karfin mutane.
Da wannan muke Allah wadai da wannan cigaban mai haƙan rijiya da ya kawo ba dama ka kunna film a gaban yaro sai yace meye Istimna'i meye Karfin Mutane.
Salisu Editor ✍️