Arewa politics

Arewa politics Arewa politics
The first with verifiable News, Breaking News, Exclusive, F**k check, investigation

"Zan yi takarar gwamna 2027 a jam'iyyar ADC domin ban ga abin tsoro a wajen Kwankwaso ba". - In ji Sheikh Ibrahim Khalil...
07/04/2026

"Zan yi takarar gwamna 2027 a jam'iyyar ADC domin ban ga abin tsoro a wajen Kwankwaso ba". - In ji Sheikh Ibrahim Khalil.

Me za ku ce?

DA ƊUMI-ƊUMI: "Kada ka ƙare kamar mahaifina" — Inji Arnold Schwarzenegger zuwa ga Donald Trump 🚨Fitaccen jarumin Hollywo...
25/03/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: "Kada ka ƙare kamar mahaifina" — Inji Arnold Schwarzenegger zuwa ga Donald Trump 🚨

Fitaccen jarumin Hollywood kuma tsohon Gwamnan California, Arnold Schwarzenegger, ya aike da saƙon gargaɗi mai ratsa jiki zuwa ga Donald Trump, inda ya ba shi labarin yadda mahaifinsa ya lalace bayan faɗuwar mulkin kama-karya na Adolf Hi**er.

Schwarzenegger ya bayyana cewa mahaifinsa, wanda ya yi yaƙi a dakarun N**i, ya ƙare rayuwarsa cikin baƙin ciki, damuwa, da shaye-shaye saboda biye wa burin Hi**er na mulkar duniya ta hanyar ƙiyayya.

A cewar sa: "Ba a cin nasara kan soyayya ta hanyar ƙiyayya—domin soyayya ce ke haɗa kan duniya. Don Allah abokina Trump, kada ka ƙare rayuwarka cikin kaɗaici da nadama kamar mahaifina."

Ku shiga shafin jaridar Hausa News domin samun ingantattun Labarai.

Iran ta kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka mai dauke da man fetur da ke ratsawa ta mashigin Hormuz da wata motar Shah...
10/03/2026

Iran ta kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka mai dauke da man fetur da ke ratsawa ta mashigin Hormuz da wata motar Shahed-136 mara matuki.

Arewa politics

YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu, ya gudanar da wata ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a Fadar Shugaban Ƙ...
27/02/2026

YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu, ya gudanar da wata ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a Fadar Shugaban Ƙasa.

An ce ganawar ta gudana ne a bayan ƙofofi rufe, inda ba a bayyana cikakken bayani kan abin da s**a tattauna ba.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Arewa politics

Mai ba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atik...
27/02/2026

Mai ba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ba’a bayan gwamnan Adamawa, Umaru Fintiri, ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Arewa politics

Idan kun samu gwamnoni 30, har da Fintiri na Adamawa da ya shiga cikinku jiya, a lissafin kuna da kuri'a 30 idan an zo z...
27/02/2026

Idan kun samu gwamnoni 30, har da Fintiri na Adamawa da ya shiga cikinku jiya, a lissafin kuna da kuri'a 30 idan an zo zabe a ranar Asabat 16 ga watan Janairu 2027.

Kuna da gwamnatin APC a kananan hukumomi shida na Abuja, da aka yi zabe kashi takwas ne cikin 100 s**a fito zabe, kashi 92 kun takuresu, suna gida basa kaunarku kuma a shirye suke su jefa muku kuri'ar faduwa a babban zabe na badi.

Ku sani fa APC falle daya ce, mutanen Najeriya basa kaunarku da yadda kuke mulki, kuma ba zasu zabeku ba domin ku ci gaba da mulkin kama-karya a kansu.

Faduwa a zaben 2027 ta tabbata LAHU A GAREKU.

TNUBU yana kuka sai Ya TAFI
REMI tana kuka sai ta TAFI
SEYI yana kuka sai ya TAFI
GBAJA yana kuka Sai ya TAFI
AKPABIO yana kuka Sai Ya TAFI
APC tana kuka Sai Ta TAFI

YA DACE JAMA'AR KASAR NAN ku sani:

A mulkin APC babu tsaro kuma babu walwala a duk fadin Najeriya.

A mulkin APC na Bola Ahmed Tinubu ba a bin ka'ida da doka.

A mulkin APC ba a buga kudi a CBN, amma ana ciwo bashi ana kashewa a wofi. Talaka na dada talaucewa, dan jari hujja yana holewa.

A shekarar 2023 da 2024 da 2025 ba a aiki da tsarin kasafin kudi da majalisa ta yi.

APC tana mulki amma ko ina a firgice take. Ta Dimauce, hankalinta ya tashi.

Da kuri'a miliyan takwas aka zabi APC da miliyan takwas sau biyu ko sau uku za a kayar da APC a 2027.

KU SHIRYA FADUWA ZABE CIKIN YARDAR ALLAH

Daga Bello Muhammad Sharada

Arewa politics

DA ƊUMI-ƊUMI: Ku Tashi Ku Kare Kanku Domin Babu Wanda Zai Kare Ku, Saƙon Gwamnan Jihar Bauchi Ga Al'ummar JiharGwamnan J...
27/02/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Ku Tashi Ku Kare Kanku Domin Babu Wanda Zai Kare Ku, Saƙon Gwamnan Jihar Bauchi Ga Al'ummar Jihar

Gwamnan Jihar Bauchi, Abdulƙadir Bala Muhammad, (Ƙauran Bauchi), ya yi kira ga al'ummar Jihar da su tashi tsaye su kare kansu daga harē-harēɲ ƴãɲ biɲdiģa, a cewarsa: "Babu wanda zai muku wannan, ku ne za ku kare kanku abin da kuke buƙata shi ne kayan aiki kuma za mu samar muku shi". In ji shi.

Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito gwamnan na bayyana hakan ne ta cikin wani bidiyo, a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban al'ummar da harin ƴan biɲḍiģa ya shafa a Jihar.

Ya ƙara da cewa maharan sun zo ne domin su kwashi tattalin arziƙin ƙwalli da mai da ke Jihar, dan haka al'umma ba za su gudu su bar musu Jiharsu ba, "Zan je Abuja na faɗa wa shugaban ƙasa, kuma na faɗa wa jami'an tsaro su samar muku kayan aiki, dole ne mu yi shirin yaƙi mu tashi mu kare kanmu". In ji gwamnan na Bauchi.

Me zaku ce?

Arewa politics

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Ƙaramar hukumar Ganye Hon. Farouk Muhammad Ganye ya sanarda ficewarsa daga jam'iyar PDP A wata sa...
27/02/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Ƙaramar hukumar Ganye Hon. Farouk Muhammad Ganye ya sanarda ficewarsa daga jam'iyar PDP

A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman a bangaren da s**a shafi harkokin sada zumunta Isa Tafida ya sanar a Yau.

Arewa politics

YANZU-YANZU: Tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami ya bayyana a kotu a yau Malami ya bayyana domin sauraron shari'arsa...
27/02/2026

YANZU-YANZU: Tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami ya bayyana a kotu a yau

Malami ya bayyana domin sauraron shari'arsa da Hukumar DSS kan zargin samunsa da makamai a gidansa da kuma ɗaukar nauyin ta'addanci, inda ake tsammanin a bada shi beli a yau.

Arewa politics

jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu rinjaye a jihohi 30 daga cikin jihohi 36 na Nigeria, lamarin da ke nun...
27/02/2026

jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu rinjaye a jihohi 30 daga cikin jihohi 36 na Nigeria, lamarin da ke nuna karuwar tasirinta a harkokin siyasar kasar.

rahotanni daga majiyoyi daban-daban na cikin gida sun bayyana cewa wannan adadi ya biyo bayan sauye-sauyen siyasa da kuma sauya sheƙar wasu gwamnoni da ‘yan majalisu zuwa jam’iyyar mai mulki, lamarin da ya kara mata karfi a matakin jihohi.

a baya, irin wannan rinjaye ya taba faruwa a lokacin da jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) ta mamaye mafi yawan jihohin kasar kafin zaben 2015, wanda daga bisani siyasa ta sauya alkibla.

shin wannan rinjaye da APC ke da shi zai kara mata karfi a zaben 2027, ko kuwa siyasa za ta sake sauya salo?

ku ci gaba da bibiyar mu domin samun cikakkun rahotanni a Arewa politics

Address

Jada

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa politics posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share