23/08/2026
Kungiyar Triple R Ta Ziyarci Jarumi Tanimu Akawu Wanda Ke Kwance A Asibiti A Halin Yanzu
Ƙungiyar ta yi tattaki daga Jihar Kano zuwa Jihar Jos domin ziyartar ɗaya daga cikin dattawan ƙungiyar, Tanimu Akawu, wanda aka amince masa ya shiga ƙungiyar.
A yayin ziyarar, ƙungiyar ta ba Tanimu Akawu tallafin kuɗi har naira miliyan ɗaya (₦1,000,000), domin taimaka masa wajen kula da lafiyarsa da kuma biyan wasu daga cikin buƙatun da s**a shafi jinyarsa.
Shugaban ƙungiyar Tripple R, Dauda Kahutu Rarara, ya tabbatar da cewa zai ɗauki nauyin kula da lafiyar Tanimu Akawu har zuwa lokacin da za a sallame shi daga asibiti.