
20/06/2023
Tattara bayanan tsaro
ASALIN HOTON, GETTY IMAGES
A kwanan baya, an jiyo Shugaba Tinubu da kansa yayin wata ziyara zuwa sabon ofishin Mai ba shi shawara kan harkar tsaro da cibiyar yaƙi da ta'addanci, ya bayyana cewa ba zai lamunci ci gaba da aiki tsakanin hukumomin tsaron ƙasar ba tare da haɗin kai ba.
Ya kuma yi gargaɗi a kan ɓoye bayanan sirri a tsakanin juna a ɓangaren hukumomin tsaron.
Masani kan tsaro Dr. Kabir Adamu ya ce rahoton wani binciken da s**a gudanar kuma s**a miƙa wa shugaban ƙasa ya nuna cewa, ɗaya daga cikin manyan kalubalen da harkar tsaron Najeriya ke fuskanta shi ne rashin tattara sahihan bayanan sirri, da tantance su, da kuma aiki da su yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa kowane bangare a cikin bangarorin tsaron ƙasar 27 yana fama da wannan matsalar, don haka, akwai bukatar mai bai wa shugaban ƙasa shawara a harkar tsaro ya bi diddigin wannan batu kuma ya sanya ido don tabbatar da samun mafita.
Baya ga waɗannan manyan matsalolin akwai kuma wasu da ake ganin suna kawo cikas sosai a harkar tsaron ta Najeriya.
Ɗaya daga ciki, ita ce zagon ƙasan ƴan siyasa waɗanda ke kawo nakasu a harkar ta tsaro.
Sau da dama tsoma bakin ƴan siyasa ta hanyar sawa ko hanawa kan haifar da matsaloli da dama.
Sai kuma batun rashin ladaftarwa a kan jami'an da s**a saɓa ƙa'ida ko s**a yi sakaci wajen tafiyar da ayyukansu.
A yanzu haka dai al'ummar Najeriya za su zura ido domin ganin kamun ludayin waɗannan sababbin manyan hafsoshi da aka naɗa.
Musamman ganin yadda aka zargi magabatansu da gazawa.
Shin ko waɗanne sabbin dabarun yaƙi da matsalar tsaro za su zo da su?