
03/03/2024
Game da saukar Shaikh Ibrahim Daurawa daga mukamin Shugaban hisba a Jihar Kano wasu malamai sun tofa albarkacin bakinsu, in da suke nuna rashin jin dadinsu da amincewar su ga haka.
Daga cikin waɗannan malamai akwai SHEIKH DR. ABDULLAH GADON KAYA in da yake cewa:
Bamu aminta da saukar Sheikh Daurawa daga mukamin Hukumar Hisbah ba, ya kamata gwamna ya nemi Malam ya ba shi hakuri don ya ci gaba da tsabtace Kano daga badala.
Sheikh Abdullah Usman Gadon Kaya, ya bayyana haka cikin wani bidiyo mai mintuna 18 da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar jiya Juma'a.
Dr. Gadon Kaya, ya bayyana irin tasirin da jagorancin Sheikh Daurawa ke da shi wajen yakar ayyukan sabo da badala a jihar Kano, da irin kokari da yake a shugabancin dukda rashin kudi da hukumar ke fama da shi.
Malamin ya bukaci gwamna da ya nemi Malam Daurawa ya a ba shi hakuri, ya kuma duba irin alherinsa a hukumar.
Haka zalika shima DR. SANI UMAR RIJIYAR LEMU yake cewa: Ana nema a mayar da Kano dandalin badala da fajirci, ana tasowa daga gari-gari da kasashe a zo Kano saboda badala.
Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo ya bayyana haka yayin gabatar da hudubarsa ta Juma'a a masallacin Al'muntada na marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam da ke Dorayi.
Malamin ya yi tsokaci dangane da irin kokarin da Hukumar Hisbah take na tsabtace Kano daga rashin tarbiyya, da bukatar goya wa hukumar baya kan irin aikace-aikacenta na alheri da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.