25/04/2025
YANZU YANZU: Rahotanni Sun Bayyana cewa ganawar Sirri da akeyi a Villa a Yau a tsakanin Kwankwaso da Tinubu, Kwankwaso ya Gindayawa Shugaban ƙasa Bola Tinubu Sharuɗa Wanda Sai An cika Waɗannan Sharuɗan Zai koma cikin jam'iyyar Apc.
1. Za'a baiwa Abba Gida Gida jagorancin jam'iyyar APC a Kano, zai zama uban jam'iyyar a Kano.
2. Dole Ganduje zai bar Shugabancin Jam'iyyar APC na Kasa.
3. Dole Abdullahi Abbas ya Sauka daga shugabancin jam'iyyar APC a Jihar Kano.
4. Za'a rushe shugabancin APC na Kano a bada rikon kwarya, yan Kwankwasiyya ne za'a ba Shugabancin Jam'iyyar na riko.
5. In anzo zaben shugabancin jam'iyyar APC na jiha, yan Gandujiyya zasu so ayi raba dai-dai din mukamai, hakan bazai samu ba, dole zasu hakura ko su bar Jamiyyar.
6. In Yan Gandujiyya s**a bar APC babu jam'iyyar da zasuje su iya kada Kwankwaso da yayumar shi ta Kwankwasiyya, saboda haka ritayar siyasa ta tabbata.
7. Kwankwaso zai zama É—an lelen Villa, zai zama shine ake saurare ba Ganduje ba.
8. Rikicin Sarakuna zai kare, Sarki Sunusi zai kasance shine Sarkin Kano. Sarki Aminu Ado Bayero dole zai hakura
9. Su Barau Jibrin zasu narke a ɓangaren Kwankwaso, saboda suna da capacity na iya cin zabe, Yan Kwankwasiyya na yanzu zasu iya zama da su Barau Jibrin da Abba Bichi.