AG Islamic Tv

AG Islamic Tv Assalamu-Alaikum
Wannan shafin Anƙirƙireshi ne don yaɗa Addin Allah da Sunnah ANNABI.(S.A.W)shafine mai zama kanta.

25/08/2026
25/08/2026

Shirin Addini da Rayuwa
Tare da sheikh Ibrahim muh’d Duguri(shugaban malamai na jibwis nhq Jos Abuja)

25/08/2026

Tambayoyi bayan Karatun littafin kaba’ir
Dr Abdulhamid ishaq umdagas

25/08/2026

Karatun littafin fatahul-majeed
Tare da Dr. sani Ibrahim mahmud
Daga masallacin jumma’a na jibwis dake kofan Alh. Hudu idiris (Jalingo)
23/8/2026

Ƙungiyar Izala Reahen Jos Ta Yi Kira Ga Musuĺmai Su Ƙara Shiga Siyasa, Ta Kuma Goyi Bayan Matsayar Sheikh Jingir Kan Mus...
23/08/2026

Ƙungiyar Izala Reahen Jos Ta Yi Kira Ga Musuĺmai Su Ƙara Shiga Siyasa, Ta Kuma Goyi Bayan Matsayar Sheikh Jingir Kan Muslim-Muslim

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis-Sunnah (JIBWIS), Hedikwatar Ƙasa da ke Jos, ta yi kira ga Musulmi da sauran ’yan Najeriya da su ƙara shiga harkokin siyasa cikin lumana da kishin ƙasa, tare da fifita adalci, amana, ƙwarewa da kishin al’umma.

Kiran ya fito ne a ƙarshen taron ƙasa kan “Ƙara Shiga Siyasa da Adalci a Matsayin Mafita ga Haɗin Kan Ƙasa da Ci Gaban Najeriya”, wanda JIBWIS ta gudanar a yau 23 ga Agusta 2026 a Saddeqa Event Centre, Jos, inda sama da mutane 350 s**a halarta daga sassan Najeriya.

A cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana damuwarta kan matsalolin tsaro da s**a addabi ƙasar, ciki har da ta’addanci, garkuwa da mutane da ’yan bindiga, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri da haɗin gwiwa wajen kare al’umma.

JIBWIS ta kuma jaddada muhimmancin adalci, daidaito, ’yancin addini da faɗin albarkacin baki, tare da yin kira ga ’yan Najeriya su guji ƙiyayyar kabilanci da addini. Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da rabon damarmaki da ayyukan ci gaba cikin adalci ba tare da nuna bambanci ba.

A wani muhimmin ɓangare na sanarwar, JIBWIS ta bayyana cewa mambobinta daga jihohi daban-daban na Najeriya suna goyon bayan duk matakin da Shugaban Majalisar Ulama’u ta JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, zai ɗauka dangane da zaɓen ƙasa na 2027, musamman batun taken “Muslim-Muslim”.

Ƙungiyar ta kuma yaba da wasu shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, noma da samar da ayyukan yi, amma ta bukaci a aiwatar da su cikin gaskiya da adalci a dukkan sassan ƙasar.

A ƙarshe, JIBWIS ta yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane, tare da yin addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

Daga Lawan Sadik

23/08/2026

Tambaya bayan karatun Riyadusalihin
22/8/2026

Address

Jalingo Tara

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AG Islamic Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category