Sautul- haqq online media

Sautul- haqq online media Ilimin kimiyya da Ilimin taurari

05/07/2026
☀️ Makomar Ranarmu (Sun)Masana kimiyya sun yi hasashen cewa nan da kimanin shekaru biliyan 5, rana za ta fara ƙarewa da ...
04/07/2026

☀️ Makomar Ranarmu (Sun)

Masana kimiyya sun yi hasashen cewa nan da kimanin shekaru biliyan 5, rana za ta fara ƙarewa da makamashinta. Za ta faɗaɗa ta zama Red Giant, inda za ta iya haɗiye Mercury da Venus, kuma rayuwa a Duniya za ta zama ba mai yiwuwa ba.

Daga baya, rana za ta zubar da ɓangarenta na waje, ta bar wani ƙaramin tauraro mai matuƙar nauyi da ake kira White Dwarf. Bayan tiriliyoyin shekaru yana ci gaba da yin sanyi, zai zama Black Dwarf.

Sai dai har yanzu babu wani Black Dwarf a sararin samaniya, domin sararin samaniya bai kai wannan tsufa ba.

Shin a fahimtarka, akwai wata dabara da kimiyya za ta iya yi domin ta sa Rana ta ci gaba da haskakawa da zafi har abada?

Ka taɓa tunanin girman sararin samaniya?A cikin Milky Way kaɗai, masana kimiyya suna hasashen akwai kusan duniyoyi tiril...
03/07/2026

Ka taɓa tunanin girman sararin samaniya?

A cikin Milky Way kaɗai, masana kimiyya suna hasashen akwai kusan duniyoyi tiriliyan 3.2 da ke kewaya taurari, sannan akwai kusan taurari biliyan 200.

Bayan haka kuma, ana kiyasin cewa akwai kusan galaxies tiriliyan 2 a faɗin sararin samaniya da ake iya hangowa.

Kai, idan haka ne, kana ganin akwai yiwuwar rayuwa a wasu duniyoyi dabam?

Proteus yana ɗaya daga cikin watannin duniyar Neptune. A cikin wannan wata akwai wani babban rami wanda faɗinsa ya kai k...
30/06/2026

Proteus yana ɗaya daga cikin watannin duniyar Neptune. A cikin wannan wata akwai wani babban rami wanda faɗinsa ya kai kusan girman Najeriya, Nijar da Kamaru idan aka haɗa su. Cikin ramin akwai duhu, kuma har yanzu ba a san ainihin abin da ke cikinsa ba. Masana suna ci gaba da bibiyar wannan rami da kuma binciken abin da yake cikinsa.

A tunaninka, mene ne yake cikin wannan rami? Kananan halittu ne? Ko arziki ne a cikinsa? Ko kuma dutse ne mai aman wuta?

🌩️ Babban Hadari Na Matsowa Najeriya!🌧️🌧️🌧️🌧️Mafi yawan sassan Arewacin Najeriya sun samu ruwan sama daga jiya zuwa safi...
30/06/2026

🌩️ Babban Hadari Na Matsowa Najeriya!🌧️🌧️🌧️🌧️

Mafi yawan sassan Arewacin Najeriya sun samu ruwan sama daga jiya zuwa safiyar yau.

A halin yanzu kuma, wani babban hadari na ci gaba da matsowa Najeriya. Ana sa ran zai fara shigowa ta Adamawa da Borno kafin daga bisani ya bazu zuwa sauran sassan Arewa.

Shin an samu ruwan sama a garinku?

Ruwan dare kuka samu kokuma a safiyar yau kuka samu ???

gajere):Wannan duwatsu da kake gani ya samo asali ne tun shekaru biliyan 4.5 da s**a wuce.Duwatsun sun so su haɗu su zam...
30/06/2026

gajere):
Wannan duwatsu da kake gani ya samo asali ne tun shekaru biliyan 4.5 da s**a wuce.
Duwatsun sun so su haɗu su zama duniya, amma ƙarfin nauyin (gravity) Jupiter ya hana su dunkulewa.
Shin ka san yadda Duniya ta samo asali kuwa?

A yau Wani Abu Mai Ƙarfi Daga Rana Na Nufar Duniyar Mu Da GuduA yau ana sa ran wani babban Solar Storm daga saman rana y...
16/05/2026

A yau Wani Abu Mai Ƙarfi Daga Rana Na Nufar Duniyar Mu Da Gudu

A yau ana sa ran wani babban Solar Storm daga saman rana ya iso kusa da duniya bayan activity na rana ya ƙaru sosai.

Masana sun ce babu wata babbar illa da ake tsammani, amma ana iya samun ɗan tangarɗa ga satellite, radio da kuma network issues.

Address

Bali Street No 4
Jalingo
660213

Telephone

+2348146969946

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sautul- haqq online media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sautul- haqq online media:

Shortcuts

Share