Haske TV

Haske TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Haske TV, TV Channel, Off Jolly Nyame Way, Jalingo.

Haske Tv is a home based family entertainment channel that displays the best of Hausa And English News, movies, shows, music and reflects on the cultural values and tradition of the Hausa heritage.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna matukar damuwarsa, kuma ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike k...
05/12/2023

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna matukar damuwarsa, kuma ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar, a yayin wani hari na jirgi maras matuƙi mallakar sojojin Najeriya.

Lamarin da ya faru a lokacin da "sojin na Najeriya s**a yi yunƙurin kai farmaki kan ƴan bindiga," k**ar yadda sojojin s**a tabbatar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata sanarwar da ya fitar a yau, Litinin.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da wasu mutane s**a taru domin gudanar da bikin Mauludi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane "bisa kuskure" tare da jikkata wasu da dama.

"Gwamnatin jihar ta aike da manyan jami’anta don tantance halin da ake ciki, da bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma ba da shawara kan daukar matakan gaggawa don rage musu radadi.

"Ina tabbatar wa ƴan jihata cewa har yanzu kariyarsu ce abin da muka fi bai wa fifiko a yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi da masu aikata laifuka a jihar." in ji sanarwar

Wadanda s**a samu raunukan za su samu kulawar gaggawa a asibitin koyarwa na Barau Dikko, inda gwamnati ta dauki nauyin kula da lafiyarsu.

Haka nan gwamna Sani ya yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da marawa jami’an tsaro da gwamnatin jihar baya a yakin da suke yi da masu aikata laifuka.

Shirin Dake Tafiya Yanzu Haka A Tashar Haske Tv
26/11/2023

Shirin Dake Tafiya Yanzu Haka A Tashar Haske Tv

Rahotanni daga filin jirgin saman Abuja na cewa kungiyoyin kwadago sun rufe t**in da ke zuwa filin jirgin saman da safiy...
09/11/2023

Rahotanni daga filin jirgin saman Abuja na cewa kungiyoyin kwadago sun rufe t**in da ke zuwa filin jirgin saman da safiyar yau, Alhamis.

Da safiyar nan ne, mutane s**a rika wallafa bidiyo na yadda motoci da masu ababen hawa s**a tsaya jingum-jingum a kan t**in. A daya daga cikin bidiyon da aka wallafa a shafin X, ana iya ganin wata motar dakon kaya daga nesa an gindaya ta a tsakiyar t**i.

Haka zalika, an jiyo kade-kade na tashi, yayin da ake iya hango wasu mutane sanye da tufafi iri daya a kan motocin da ke nesa.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya shaida wa BBC cewa mambobinsu sun rufe t**in shiga filin jirgin saman na Abuja da kuma hana duk wani jirgin sama da ke da niyyar tashi zuwa jihar Imo.

Haka kuma wata sanarwa da babban sakataren NLC, Kwamared Emmanuel Ugboaja ya fitar ta ce matakin ya hadar da filin jirgin sama na Lagos.

Ta kuma ambaci matakin da 'yan kwadagon ke dauka a dambarwarsu da gwamnatin jihar Imo.

A ranar Laraba dai 8 ga watan Nuwamban 2023, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC s**a fara wani yajin aiki, wanda s**a sanar da rufe duk wasu harkokin samar da lantarki da na sufurin jiragen sama a jihar ta Imo.

Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zargin da kungiyar NLC ta yi wa gwamnan jihar Hope Uzodinma da hadin bakin 'yan sanda wajen k**a shi tare da dukan sa. 'Yan kwadagon daga bisani sun nuna hoton shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da idonsa na dama a kumbure.

Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.Haka zali...
20/09/2023

Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Jam'iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir, bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 18 ga watan Maris na 2023.

Kotun ta bayyana wannan hukunci ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro.

Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugabar kotun mai alƙalai guda uku.

Muna taya Dukkannin Mabiyan Murnar Ranar Hausa Ta Duniya
26/08/2023

Muna taya Dukkannin Mabiyan Murnar Ranar Hausa Ta Duniya

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.A cikin wata sanarwa da ya ...
21/08/2023

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin rage irin wahalhalun da tsadar kuɗin makaranta ke haifarwa ga al'ummar jihar.

Sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari na kuɗin makaranta da ɗalibai ke biya a jami'ar jihar Kaduna, wato KASU.

Haka nan an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.

Bugu da ƙari sanarwar ta ce an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a Kwalejin ilimi ta jihar da ke Gidan Waya.

Yayin da aka yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai masu karatun babban difiloma ke biya a Kwalejin koyar da harkokin lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi, inda su ma masu karatun difiloma za su samu ragin kashi talatin cikin ɗari.

A ƙarshe sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin koyon jinya ta jihar.

Ministan wutar lantarki - Adebayo AdelabuMinistan harkokin tattalin arzikin teku - Adegboyega OyetolaMinistan kwadago da...
21/08/2023

Ministan wutar lantarki - Adebayo Adelabu

Ministan harkokin tattalin arzikin teku - Adegboyega Oyetola

Ministan kwadago da daukan aiki - Simon B. Lalong

Ministan harkokin cikin gida - Bunmi Tunji-Ojo

Ministan Babban Birnin Tarayya - Nyesom

Wasu ministocin da s**a sha rantsarwa yanzuKaramin Ministan Noma da Abinci - Aliyu Sabi AbdullahiMinistan yada labarai d...
21/08/2023

Wasu ministocin da s**a sha rantsarwa yanzu
Karamin Ministan Noma da Abinci - Aliyu Sabi Abdullahi

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a - Muhammad Idris

Ministan kula muhalli - Ishak Salako

Ministan kudi da hadin kai na tattalin arziki - Wale Odun

Ministan sadarwa da kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital - Bosun Tijani

Wasu karin ministocin da aka rantsarMinistar yawon bude ido - Lola Ade-JohnMinistan harkokin 'yan sanda - Imaan Sulaiman...
21/08/2023

Wasu karin ministocin da aka rantsar
Ministar yawon bude ido - Lola Ade-John

Ministan harkokin 'yan sanda - Imaan Sulaiman-Ibrahim

Karamin ministan lafiya da walwalar jama'a - Tunji Alausa

Ministan Karafa- Shuaibu A. Audu

Karamin Ministan Ilimi - Yusuf T Sununu

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane - Abdullah T. GwarzoMinistar fasaha da al'adu - Hannatu MusawaMinistan gidaje da ...
21/08/2023

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane - Abdullah T. Gwarzo

Ministar fasaha da al'adu - Hannatu Musawa

Ministan gidaje da raya birane - Ahmed M. Dangiwa

Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya - Mairiga Mahmud

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki - Atiku Bagudu

Address

Off Jolly Nyame Way
Jalingo
660213

Telephone

+2349155191791

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Haske TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Haske TV:

Share

Category