22/04/2025
Dr. Nicolas Kokkalis, CEO Pi Network, tare da team dinsa sun fitar da sanarwa a daren nan cewa:
Second migration da za'a yi nan gaba zai kunshi referral bonus da mutane s**a samu daga downline dinsu wadanda s**a tsallake KYC. Migration na farko da yanzu haka ake kanyi ana yin sa ne gwargwadon Mining din da kayi kai daya, da kuma Lockup duration tare kuma da security circle performance na Pioneers.
A cikin jawabin da Core team s**a fitar yau sun ce har yanzu ba'a kammala migration na farko ba, da zaran an kammala za'a shiga second migration wanda a lokacin za'a turawa mutane referral bonus da s**a samu.
Third migration kuma zai kasance duk bayan wata-wata (monthly) ko kuma quatrtelly (duk bayan wata uku-uku) ko kuma yearly, kamar yadda core team s**a sanar.
Third migration zai kun shi abubuwa uku da za'a kula dasu a lokacin;
1. Pi din da aka tara su bayan first migration da kuma sabon Lockup da user ya canza.
2. Migration ga sabbin Pioneers.
3. Validators da s**a yi aiki a lokacin KYC, wadanda s**a taimaka wajen tantance mutane daban daban daga kasashe masu yawa.
Abinda aka tura maka a yanzu adadin Pi din da kayi mining ne kai kadai ba tare da Bonus daga ko'ina ba. Alamu suna nuna anyi kusa a kammala first migration, an tantance mutane kusan miliyan 15, kuma anyi musu migration.
Yayin da sauran miliyoyin mutanen ake zaton basu nuna wata alamar suna raye ko suna da niyyar yin KYC don a tantance da kuma yi musu migration nan gaba.
Alamu suna nuna idan an fara second migration duk wanda bai yi KYC ba zai iya rasa Pi dinsa musamman daga cikin wadannan s**a fara yin Mining Pi daga 2019 zuwa 2024.