Usman Idris Usman

Usman Idris Usman No father chooses to die and leave his children to fight for themselves. May allah grant all our late parents jannah
🤲

27/05/2025

Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji
An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce
Annabi (SAW) ya ce:

(1) Ranar daya ga watan zilhijja ita ce ranar da Allah (swt) ya gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da shi.

(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada .

(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) ya ba shi haihuwa duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) zai karbi adduo’insa.

(4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu.

(5) Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) zai kare shi daga munafunci ko azabar kabari.

(6) Ranar shida ga Zilhijja ita ce ranar da Allah (SWT) ya yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai dube shi da rahama, kuma ba zai azabtar da shi ba.

(7) Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude suba har sai wadannan kwanaki goma sun wuce. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai rufe masa kofofi talatin na tsanani a rayuwarsa a buda masa kofofi talatin na sauki.

(8) Ranar takwas ga Zilhijja ita ce ranar da ake cewa, ranar tarayya. Duk wanda ya azimci wannan ranar, babu wanda ya san adadin ladansa sai Allah.

(9) Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar
hawan Arfa. Allah yana gafartawa duk Alhazan dake wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah yana gafarta masa zunibinsa na shekarar data gabata, da kuma shekarar da ke tafe.

(10). Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya. Duk wanda Allah ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da iyalinsa. An so wanda zai yi layya da wanda ba zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan an dawo daga sallar idi, ya ci abinci ko wani abu daga
cikin layyarsa. Allah zai ba shi lada wacce ta fi Dutsen Uhud girma da nauyi. Kuma ana so yaraba namansa kashi uku.

Kashi na farko sadaka, kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin
iyali.

Allah Ya Bamu Ikon Azumtar Dukkan Wadannan Ranakun, kuma ya sadamu da falalar da yatanadar ga masu Ibada awadannan kwanaki. Ameeen.

09/05/2025

Wayewa itace mutun ya san mu’amala kuma ya iya ta. Ya iya amfani da kwakwalwa fiye da zuciya. Ya iya amfani da hikima fiye da kwarewa.👌

01/05/2025

Ya Allah,
Ya Rahman,
Ya Rahim,
Ya sallam,
Ya Maliku,
Ya Hakeem,
Ya Kareem,
Ya maliqulmulk
Ya zuljalalu wal iqram
Ya hayyu Ya kayyu ka biya mana bukatunmu na alkairi badon mu ba.🤲

25/04/2025

Ba wanda ba zai rayu cikin aminci ba sai wanda ya daura wa kan sa rayuwar da ba ta sa ba.👌

Masha Allah Taqabbalallahu minna wa minkum eidil Mubarak Alaina wa alaikum.👏From police headquarter jalingo
30/03/2025

Masha Allah

Taqabbalallahu minna wa minkum eidil Mubarak Alaina wa alaikum.👏

From police headquarter jalingo

13/02/2025

Ka da labarin wani ya tsorata ka, domin kaddarar ku daban ce, kawai ka dau darasin labarin sa kaci gaba da yiwa Allah fadanci.👌

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Umar Yahya Abubakar, Umar Farouq Mallamcy, Salix M Mashi,...
03/01/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Umar Yahya Abubakar, Umar Farouq Mallamcy, Salix M Mashi, Ibrahim Mukhtar Ajit, Haruna Garba Koko, Abubakar Goga Anfield, Fatima Umar Hassan, Deeni Wali Kano, Aminu Hussaini Gusau, Maimuna Garba, Muhammad Adamu Tela, Mai Sunan Malam, Ibrahim Adamu Usman, Abdulrahman Hassan, Abdullahi Ameena, Khalid Dalhatu, Abdullahi Shehu Al-afasy, Umar Sani Jibrin Al'alawy, Rabia Shehu, Maryam Tambuwal, Maryam Mala, Yusuf Guyson Kurah, Itz Ameenu Vandersar, Murtala Istandwith Buhari, ᎡᎬᎪᏞ ᏆᏚᎪᎻ, Itz Yusuf Tarazu, Ishaq Hassan, Hassana Edreeth Ummu Irfern, Nāzēēf Danjøømer Eåsērh, Ya'u Muhammad Coca-cola, Lyfêstylê Så Må Dø, Abba Limson, Jabir Excellency, Suleeman Danjimma I'm so grateful 👏

26/12/2024

Ka dena jin haushin mutane don basu taimake ka ba, Taimako ganin dama ce, Baka san yadda wasu mutanen suke takurawa kan su don ganin sun taimakeka ba. Ka mike tsaye kawai ka yarda da Allah, Kuma kataimaki kanka shine Allah zai taimakeka.👌

A lokacin da wani yake sauka, lokacin wani yake hawa - shekaru ko mataki ko matsayiTabbas wannan hoto yana dauke da dara...
26/12/2024

A lokacin da wani yake sauka, lokacin wani yake hawa - shekaru ko mataki ko matsayi

Tabbas wannan hoto yana dauke da darasi mai karfi.

22/12/2024

Dai dai kibar mace, dai dai samun kwanciyar hankalin mai gidanta, amma kaga wadannan masu k**a da sandan rake Ina rabaka dasu dan uwa.🤦🏻‍♂️🥱

19/12/2024

Duk lokacin da ka dauki hassada abokin rayuwar ka to ka kulla alaka kenan da bakin ciki har abada.

Allah ka tsare mana zukatan mu.🤲

Address

Jalingo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usman Idris Usman posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share