15/10/2025
Gonga News Sabbin Labarai daga Najeriya
1. IMF ta yi gargadi kan fitar da haramtattun kuɗi daga Najeriya
Ƙungiyar IMF ta bayyana damuwa kan yawaitar fitar da kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba daga Najeriya, tana mai cewa hakan na iya zama babban barazana ga cigaban tattalin arzikin ƙasa.
2. Gwamna Abdullahi Sule ya tona batun barazanar Boko Haram a Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa, Engr. Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hukumomi sun gano wata ƙungiya da ake zargin tana da alaƙa da Boko Haram da ke yunkurin shiga yankin Nasarawa.
3. Gwamnan Edo ya umurci ma’aikata su nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu
Gwamna Monday Okpebhola na Edo ya umarci ma’aikatansa su sanya hular shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wuraren aiki, a matsayin alamar goyon baya ga gwamnatin tarayya.
4. Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya kan rasuwar Fasto Uma Ukpai
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan mutuwar babban malamin addini, Fasto Uma Ukpai, wanda aka sani da tasiri wajen wa’azi da addu’o’in ƙasa.
5. Rundunar ‘Yan Sanda ta kai farmaki Abuja, ta hallaka ɗan ta’adda “Mai Duna”
‘Yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun kai samame inda s**a gano mabuyar ɗan ta’adda mai suna “Mai Duna”. An samu musayar wuta kafin a kwato makamai da kayan aikinsa.
6. Bashin Najeriya ya kai tiriliyan 149 Gwamnati na shirin sabon bashi
Rahotanni sun nuna cewa bashin da Najeriya ke bin yanzu ya kai Naira tiriliyan 149, yayin da gwamnatin tarayya ke shirye-shiryen ɗaukar sabon lamuni domin cike gibin kasafin kuɗi.
Gonga News – Muryar Mutane Gaskiya.
Jalingo, Taraba State | www.gonga.ng