19/10/2025
ZUWAGA GWAMNTIN NIGERIA
Bai buya ga duk Wani Mutum Mai hankali Wanda yasan Kalmar mutumtaka ba irin zalunci da gwamnatin kasarmu keyi akan SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY H da almajiransa Wanda bai buya ga Al'umma ba cewa gwamnatoci da s**a gabata sunyi abunda s**ayi sannan s**a gadarwa Mai ci yanzu wato gwamnatin dake gudana karkashin Bola Ahmed Tunubu.
Wanda sun kashe sun daure Kuma suna takan zaluncin kamar yadda Gwamnatocin baya s**a gadar musu a yanzu maganar da mukeyi shine akwai Yan uwanmu masu rauni a hannun wannan gwamnatin Wanda ta dauresu ba bisa qa'ida ko Wani laifiba ta rabasu da iyalansu ga ciwuka Babu magani ba abinci sun daure Maza da mata harda wadanda s**a kashe basu bamu gawarwakinsu munyi musu janaza kamar yadda addini ya tanadar ba Kuma wai ance shi shugaban kasa Musulmi ne ko baisan haqqin mamacibane, mene gwamnati take nufine?
To Muna kira da babbar murya Ku Sako mana Yan uwanmu mu kaisu asibiti ayi musu jinya, sannan ku bamu gawarwakin shahidanmu muyi musu sutura mukaisu makwancinsu kukuma sakomana Yan uwa da abokanmu da basu muku laifin komaiba.
Kukuma Al'ummar kasata Nigeria ban cire kowaba kusani cewa wannan abunda akeyi akan jagoranmu Sayyid Zakzaky H dakuma almajiransa zaluncine shirun da kukayi Kuma ya nuna yardane da amincewarku ga hakan sbd haka Kuna goyon bayan azzalumai ne Annabi SAWW yace duk Wanda ya goyi da zalunci to dashi akayi sbd haka kusan matsayinku cikin Al'ummar ku da kuke tare da ita.
Labbaka ya Al-Zakzaky
Mu bama goyon bayan zalunci da azzalumai Kuma baza mu taba goyon bayansuba.
Dan Allah yan uwa a yada sakon yaje inda ya dace.🙏
✍️ Mbfudiyyah
mana Yan uwanmu
jikkunan shahidanmu
marasa lafiyarmu
zalunci
ga gwamnatin Nigeria