08/09/2025
𝗬𝗔𝗗𝗗𝗔 𝗔𝗞𝗘 𝗦𝗔𝗟𝗔𝗧𝗨𝗧-𝗧𝗔𝗦𝗕𝗜𝗛 ✅
ANNABI SAW yace da Baffansa Abbas ya Baffa na Shin bana bazan baka wata kyauta ba shin bakaso in baka wadansu Abubuwa guda goma wadanda idan ka Aikata Wannan Sallar Allah zai gafarta maka.
1-Nafarkonsu dana karshe
2_Nada da Sabo
3_Na Ganganci da Kuskure
4-Babbansu da karaminsu
5-Na boye Dana bayyane
ANA NUFIN ZUNUBBAI INA FATAN MUN GANE?
YADDA AKEYIN SALLAR
-Anayin Raka'oi guda Hudu (4)
-A kowace Raka'a Ana karanta fatiha da sura
-Bayan kagama karanta sura da fatiha kafin kayi Ruku'u Zaka Fadi "Subhanallah ,Walhamdulillah,wala"'ilaha illallah,Wallahu Akbar Sau Sha biyar(15)
-Sannan Acikin Ruku'u Zaka maimata sau goma(10)
-Idan ka d**o daga Ruku'i kafin katafi sujuda Zaka maimata sau goma (10)
-Aciki sujuda Zaka maimata sau goma (10)
-idan ka d**o daga Sujuda Zaka maimata sau goma (10)
-Idan kasake komawa Sujuda Zaka maimata sau goma (10)
-Idan ka d**o daga Sujuda kafin ka miqe Zaka maimata sau goma (10)
WANNAN ITACE SALATUL TASBIH DUK WANDA YA AIKATA TA ALLAH ZAI GAFARTA MASA ZUNUBBAN SA.
ANNABI SAW yace da Abbas "idan Zaka iya ka AIKATA TA:
1-Kullum
2-Ko Kuma duk sati
3-Ko Kuma duk wata
4-Ko Kuma duk shekara
5-Ko Kuma koda sau daya(1) ne a Rayuwar ka.
SUNANI ABI DAWUD 1297(Albani ya ingantasa)
YA ALLAH KA DATAR DAMU DUNIYA DA LAHIRA🤲
Copied