
13/08/2025
Alhamdulillah!
Muna farin cikin sanar da cewa wata baiwar Allah daga cikin garin mu na Jega Allah ya azirta ta da karɓar addinin musulunci, Kuma ta zaɓi suna Maryam.
Cikin ikon Allah da kaddarawarsa Bayan musuluntar ta sai ta samu Wanda yake sonta da Aure, Wanda za'a Daura auren Ranar Assabar 16/08/2025 da Misalin 11:00pm a Masallacin Gobirawa Jega.
Kamar yadda kowa ya sani, aure ibada ce kuma yana zuwa da ɗawainiyyia daban-daban.
A matsayinmu na ‘yan uwanta musulmai, muna son mu taya ta farin ciki tare da tallafa mata domin hidimomin aure su gudana cikin sauƙi.
Ga wanda Allah ya bawa iko zai iya bayar da gudunmuwarsa ta hanyar kuɗi ko kaya, ko ɗaukar nauyin wani abu.
Kasani duk gudunmuwar da daka bayar — ko kaɗan ce ko mai yawa ce — zata zama sadaƙatul jariyah a gareka, kuma zai taimaka wajen gina sabuwar rayuwar wannan yarinyar.
•Domin bada gudunmuwa
Account: 0106314318
Bank: Union Bank
Name Ima Ullah Women MPSC
•Domin Karin Bayani sai a tuntubi wannan Numbar 09066296914
Allah Ya saka da alkhairi, Yakara daukaka musulunci da musulmai, Allah ya sanyawa wannan Auren Albarka 🤲