22/09/2022
Local Government Autonomy Bill: Wannan doka ce da ake ƙoƙarin kafawa a gyaran kundin ƙasarmu, Nigeria. Tsarin zai bai wa ƙanan hukumomi samun damar cin gashin kansu a dokance, k**a daga kan kasafin kuɗi da sauran shirye-shirye.
Mutanen da suke da alhakin yarda da kuma amincewa da wannan doka, wadda zata taimaka ainun wajen samun sauƙin tafikar da tsare-tsaren gwamnati, sun haɗar da ƴan majalissun jiha (Members House of Representatives).
A wannan dalilin ne muke miƙa roƙon bararmu a garesu domin su yarje wa wannan doka domin samar da sauƙi ga talakawa da kuma sama musu kusanci da shuwagabannin su a gwamnatance.
Mun yarda cewa ƴan majalissun mu na jihar Jigawa jajirtattu ne wajen tabbatar da cewa waɗanda suke wakilta a majalissar jiha sun samu cigaba mai ɗorewa. Mun kuma san cewa a baya sunyi abubuwan cigaba a yankunan da suke wakilta.
Saboda haka, muna da buƙatar samun wasu daga cikin gagaruman cigaban da s**a kaiwa yankunan su wanda ake alfahari da su har ila yau.
Duk wanda yake da sha'awar taimakawa da wannan bayanai, za a iya tura mana da su a email address ko kuma lambar wayar mu da muka samar a wannan hoto.
([email protected] - +2347062822399)
Share Across Please.