
16/09/2025
Shin ka taɓa jin ciwon ciki da ba ya ƙarewa? Ka taɓa tashi da safe kana jin wuta na ci a cikinka?
Wannan na iya zama ulcer; wata cuta mai saurin yaduwa wadda take ɓata rayuwa, tana hana bacci, kuma tana iya haifar da barazanar mutuwa idan ba a dauki mataki ba. Abin takaici shi ne, dabi’unmu na yau da kullum ne ke buɗe ƙofa ga wannan ciwo mai zafi da haɗari.
MENENE ULCER/GYAMBON CIKI?
Ulcer ciwo ne da ke ɓarke a bangon ciki ko hanji, wanda yawanci ke faruwa saboda yawan acid ko lahani ga garkuwar ciki. Yana iya zama gastric ulcer (a ciki) ko duodenal ulcer (a hanji).
DABI'U 7 DAKE HAIFAR DA ULCER:
1. Cin abinci mara lokaci:
Mutane da dama suna wuce lokaci ba tare da sun ci ba. Wannan yana ƙara acid a ciki, wanda ke cin jikin ciki.
2. Yawan shan shayi mai ƙarfi ko kofi:
Caffeine na ƙara yawan acid, wanda zai iya buɗe hanya ga ulcer.
3. Shan sigari da barasa:
Waɗannan na rage kariyar da ciki ke da ita, suna buɗe hanya ga ciwo da zubar jini a ciki.
4. Rashin bacci da damuwa (stress):
Damuwa yana sa jiki ya ƙara acid da kuma rage narkewar abinci, wanda ke ƙara haɗarin ulcer.
5. Yawan shan magungunan NSAIDs:
Magunguna irin su ibuprofen, diclofenac da sauransu suna hana ciki kare kansa daga acid.
6. Rashin tsaftar abinci:
Bakteria irin su Helicobacter pylori na haddasa ulcer ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwa.
7. Ci gaba da watsi da alamun farko:
Yawan jin zafi bayan cin abinci, kaikayi a ciki, amai ko zafin ƙirji na iya zama alamar farko.
WATSI DA WADANNAN DABI'U NA IYA HAIFAR DA:
- Zubar jini a ciki
- Rami a bangon ciki (perforation)
- Ciwon da ba ya warkewa
- Rashin iya aiki da walwala
Idan ka canza wadannan dabi’u, zaka iya kaucewa wannan cuta mai ban tsoro. Ka rika cin abinci akan lokaci, rage damuwa, guje wa shan magani ba tare da shawara ba, da kuma kiyaye tsafta.
KATUNA
Ciki mai lafiya shi ke kawo natsuwa. Amma ulcer na iya ruguza komai.
Ka zabi lafiya, ka guji dabi’un da ke buɗe ƙofar ulcer.
SMSHealthWise,