Jakadiyar Jigawa

Jakadiyar Jigawa JAKADIYAR JIGAWA, ALFAHARIN KOWA
GIDAN JARIDA DAIDAI DA ZAMANIN YAU.

Lionel Messi ne kawai ya zura kwallaye da bugun tazara [Free-kick] a manyan gasannin: 🏆 UEFA Champions League 🌍 FIFA Wor...
21/06/2025

Lionel Messi ne kawai ya zura kwallaye da bugun tazara [Free-kick] a manyan gasannin:

🏆 UEFA Champions League
🌍 FIFA World Cup
🏆 FIFA Club World Cup
🇦🇷 Copa America

IN AJALI YA YI KIRA...! Su kuma waɗannan ma'auratan da ke birnin Ado-Ekiti na jihar Ekiti ajalinsu a hannun junansu yake...
19/02/2025

IN AJALI YA YI KIRA...! Su kuma waɗannan ma'auratan da ke birnin Ado-Ekiti na jihar Ekiti ajalinsu a hannun junansu yake, yayin da matar ta yanke wa mijinta mazak*tarsa yayin da shi kuma ya buge ta da wani madoki hakan ya sa take s**a zube ƙasa gabaɗayansu s**a mutu. Yanzu haka dai babu wanda ya rayu a cikinsu. Tuni dai kafafen sada zumunta na yankin kudancin ƙasar nan ya ɗauki ɗumi bayan bayyanar wannan abu.

INNALILAHI WA'INNA ILAIHIN RAJI'UN! Yanzu muka samu labarin Allah ya yi wa Ɗan Masanin Ringim rasuwa, Alhaji Lawan Tahir...
08/02/2025

INNALILAHI WA'INNA ILAIHIN RAJI'UN!

Yanzu muka samu labarin Allah ya yi wa Ɗan Masanin Ringim rasuwa, Alhaji Lawan Tahir.

Muna addu'ar Allah ya yi masa rahama.

KA JI RABO: An karrama Prakriti Malla daga Nepal a matsayin wacce ta fi kowa iya kyakkyawan rubutu na hannu.Kuna ganin t...
08/02/2025

KA JI RABO: An karrama Prakriti Malla daga Nepal a matsayin wacce ta fi kowa iya kyakkyawan rubutu na hannu.

Kuna ganin ta cancanta?.

IYAKAR ƘASASHEN AMURKA DA MEXICOMazauna Naco, ta jihar Arizona a ƙasar Amurka da mazauna Naco, ta kasar Mexico suna buga...
08/02/2025

IYAKAR ƘASASHEN AMURKA DA MEXICO

Mazauna Naco, ta jihar Arizona a ƙasar Amurka da mazauna Naco, ta kasar Mexico suna buga wasan kwallon raga a kan shingen iyakar ƙasashen biyu, Amurka da Mexico a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 2015.

Daga: Dr. Muhammad Cisse

WATA SABUWA: An k**a wani likita da ya soki shugaban ƙasar Burkina Faso 🇧🇫 Captain Ibrahim Traoré bisa zargin sa da rash...
08/02/2025

WATA SABUWA: An k**a wani likita da ya soki shugaban ƙasar Burkina Faso 🇧🇫 Captain Ibrahim Traoré bisa zargin sa da rashin ɗaukar matakan yaƙi da ta'addanci, an kuma kai shi fagen daga bayan ya samu horo.

Rahotanni sun ce shugaban ƙasar ya ce a bar shi ya bayar da gudunmawa kai tsaye wajen yaƙi da ta’addanci, tunda ya yi imanin ya fi jami’an tsaro sanin aikinsu.

Yaya kuke gani idan aka fara haka a Najeriya, ko ƴan ta'adda za su wanye lafiya?.

YABON GWANI...!: Hon. Dr. Makki Abubakar Ƴalleman ke nan yayin da sabbin ƴansandansa da ya sama wa aiki kimanin su 137 d...
01/02/2025

YABON GWANI...!: Hon. Dr. Makki Abubakar Ƴalleman ke nan yayin da sabbin ƴansandansa da ya sama wa aiki kimanin su 137 daga cikin ƴaƴan talakawan da yake wakilta da wasu tsiraru daga sauran ƙananan hukumomin jihar Jigawa, yayin da suke karrama shi da lambar yabo. Lalle wakilci ya yi rana.

Gaskiya an tashi kaina a nan! 😊

29/01/2025

Martanin Ordinary President, Ahmad Isah kan sabon batun da ya taso na Hussaina matar Seaman Abbas da ƴan'uwansa.


28/01/2025

Ƙasar Najeriya ta zama helkotar ƴan bilicin ta duniya saboda yawan amfani da mayuka da sauran abubuwan ƙara hasken fata. Lalle mun fara samun cigaba a ƙasar nan!

27/01/2025

Bayani na ilimi da adalci kan Qur'anic Comference daga bakin Sheikh Muhammad S Khamis Abu Haisam HafizahulLAH. - Live via https://onestream.live

LABARAN RANA: Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya lamunce a gina sabuwar kwalejin kimiyya da fasa tare da saka mata sunan...
21/01/2025

LABARAN RANA: Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya lamunce a gina sabuwar kwalejin kimiyya da fasa tare da saka mata sunansa wato (Bola Ahmed Tinubu Polytechnic, Abuja) (BAT-POLY, Abuja), wanda ya umarci ministan Abuja Nyesom Wike da ya sama mata gurbi a Gwarimpa da ke birnin tarayya Abuja.

Me za ku ce?.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, ya ce gwamnatinsa za ta samar da kamfanin bayar da bashi ga mutane da kuma masana...
01/01/2025

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, ya ce gwamnatinsa za ta samar da kamfanin bayar da bashi ga mutane da kuma masana'antu

Me za ku ce?.

Address

Jigawa
Jigawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jakadiyar Jigawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jakadiyar Jigawa:

Share