04/08/2026
Wataƙila yau ka fara jin wannan amma da yawa basu san cewa wannan tsutsar itace ke rikeɗewa ta zama Malam buɗa littafi ba, butterfly 🦋. Ana kiran ta da caterpillar.
Farkon yadda abin ke faruwa shine Malam buɗa littafi suna kwai a jikin tsirrai, bayan kwan sun kyankyashe sai su canja zuwa tsutsotsi, larva (caterpillar), daga nan sai su ƙara rikiɗewa zuwa wata halitta mai k**a da kwanso wanda ake kira da pupa (chrysalis a kimiya).
A mataki na ƙarshe, Malam buɗa littafi yana fita daga cikin kwanson pupa ne. Idan ya fita, zai jima a zaune yana shan iska domin ya samu ƙarfin tashi k**ar yadda ka ke gani a hoto na biyu.
Ba wannan ne ma babban abin al'ajabi a haihuwar Malam buɗa littafi ba, babban abin shine kusan duk jinsin Malam buɗa littafi akwai irin tsirran da shi kaɗai ne yake yin kwansa a kai. Ma'ana, akwai jinsin Malam buɗa littafi ɗin da akan tsirran Sabara kawai su ke zuba kwan su domin tsutsar caterpillar shine abincin ta. Wasu kuma a kan itacen Kargo kawai su ke yin kwansu domin tsutsar Kargo shine kaɗai abinci ta.