Twins hausa media

Twins hausa media Jarumi

You are not just a regular boss. You are the person that inspires us every day to keep pushing on for success. Happy bir...
15/03/2023

You are not just a regular boss. You are the person that inspires us every day to keep pushing on for success. Happy birthday to one the most perfect person I have seen! I can't thank you enough for your mentorship and your advocacy. ... enjoy your day

10/03/2023

BAKIN DUHU___3

(dark black)
_______________
Budar bakinta kai Dan Allah malan kadaina wasa dani to wlh yau watan ka daya da kwana biyar kenan bansaka a idanuwa naba.

Kodai kafara shaye shaye ne zakace jiyama kazo guna a dimauce na kalli bilki tare da cewa Dan Allah bilki da gaske kikemin wqnnan maganar ko wasa ce adaidai lokacin Dana yimata wannan maganar kenan saiga salma zata wuce budar bakin salma lokacin da mukayi idol biyu lah yaya dama kana gari ka boye kodai ka koma ne?

Ai kuwa saina yarda da maganar bilki tabbas gaskiya ce to amma tayaya hakan zata faru kenan baccin da nake ganin na kwanta jiya shine nayi har wa'yannan kwanakin s**a shude amma nake ganin kamar nayi kwanan "yan awoyi lalle ko idan hakane yakamata na koma gida na binciki kaina.

Cikin yanayin raha na shashantar da bilki tare da cemata dama asane nake wasa muka Dana dimin vana son tasan halin da nake ciki.

Nantake na baro wajenta zuciya ta cike da tsoro da wasi wasi na iso gida kai tsaye na wuce gun littafin nan domin shine babban abin zargina na farko akan wannan abin da yake faruwa dani.

Da isata gunsa kawai hannu nasaka da niyar daukar sa amma sai naji tamkar wata duniya nake shirin dauka tsabar nauyin sa harsaida naji gabar hannuna ta amsa cikin yanayin mamaki naja da baya Ina kallon sa Wanda kallon Dana yimasa ne.

Yasa nagane vangon littafin ya canza daga jah zuwa vaki ai kuwa sai wani irin tsoro ya kamani nantake sai gumi ya cika fuskata kafafuwa na s**a dauki rawa.

06/03/2023

BAKIN DUHU___2
(dark black)
______________

Ina cike da mamakin yadda wannan littafin dake cikin aljihuna yabar jikina kafin safe nayi duk wani tunani na amma nakasa gano wannan abin mamakin mai cike da tsoro amma a wannan lokacin sai allah yasanyawa zuciya ta kokwanton ni na ajiyesa kila duk da zuciya ta bata yarda da hakan ba.

Saina cirewa zuciya ta ko wane tsoro na gudanar da sallah ta""ta asubah bayan nadanci abinci saina nufi gidan su bilkisu abinka da mai nema baya zuciya duk da wulakancin da bilki kemin amma nakasa mantawa da ita.

Da isata kofar gidan nasu sainaci karo da wani sabon Abu a idanuwa na wato yadda aka canzawa gidan su bilkisu style tare da canza masa fanti

Aiko a wannan lokacin sai na fada dogon tinani tayaya hakan zata faru jiya fa har wajen karfe 9:00pm Ina wajen nan kuma ni banga alamun za'a fara wani aiki ba mai K**a da wannan.

Kodai ba gidan su bilkisu nazo ba amma tayaya zan bata gidan su bilki tabbas nan ne Ina wannan tunanin ne saiga wani Yaro yazo wucewa kamar yadda nasaba saina tare sa na aikasa kiran bilkisu yadda yaron ya shiga gidan tare da cemin yayar ya kara tabbatar min lalle nanne.

Dama nasaba aduk lokacin Dana aika kiran ta nakan shafe fiye da 2 hours inajiranta amma duk da hakan sai yazan bana iya ganin dadewar ta domin irin sonda nake mata.

Da zuwanta guna sai kuwa na Kara fadawa wani dogon mamakin da yafi na farkon domin bilkisu atako Ina ta canza ta Kara kyau ta kuma Kara jiki da haske kamar wadda nafi shekara biyar banganta ba sai yanzu.

Budar bakin ta lokacin da take isowa wajena hmm sai yanzu aka tuna dani kenan?

Wai kuma ahakan sona ake cikin yanayin sakin fuska na kalli bilkisu nace bangane abinda kk son cewa ba kullun fa sai nazo gunki duk da irin wulakancin da kk min bana gajiya wani irin kallo tayamin tare da cewa hmm Adah kake zuwa guna kullun amma yanzu kadaina Nina zatama baka gari.

Budar bakina gunta Habah bilkisu jiya fa muka rabu dake harkin manta wulakancin da kk min budar bakin ta.

05/03/2023

BAKIN DUHU__1

( dark black)
________________
Tafiya kawai nakeyi misalin karfe 2:30pm na dare kunnuwa na sanye da earphone 🎧 Ina sauraren music.
____babu abinda ke cikin zuciya ta hadi da kunshe araina tamkar bakin cikin da ta cusamin arai.

Tafiya kawai nake ni kadai batare da kowa ba kamar yadda bana ganin kowa gaba na ko baya na banyi mamakin ganin hakan ba domin garin Dan karamin kauye ne.

Yau inada 3 days acikin sa sunan garin nazo ne sanadiyar bilkisu amma ni Dan asalin maiduguri ne.

Yalkabu kuwa wani kauye ne dake jahar .

Kwatsam Ina cikin wannan tafiyar ne sai idanuwa na s**a ci karo da wani Dan karamin littafi adaidai gindin wata bushiyar kuka.

Kai tsaye saina dunfari gurin da yake domin na dauka Nantake sai tunani yazomin wannan bishiyar tayi kaurin suna Wajen daukar miyagun aljanu.

A wannan lokacin sai zuciya ta"ta sare da daukar wannan littafin nayi niyar barin sa' kamar sihiri sai naji zuciya ta takamu da son sanin abinda ke cikin wannan littafin abinka da rubutacciyar kaddarar mutun kawai na dauka na sakashi a aljihuna.

Koda na shiga dakina idanuwa na cike da yanayin bacci kai tsaye kan gado na 'na fada ko takalma na bansamu cirewa va wannan ranar itace ta farko Dana kwanta bacci batare da kayan bacci ba.

Domin bantaba jin bacci irin wannan ba arayuwa ta kamar ka 'kifta ido ka bude sai naji kamar anshafi fuskata da wani Abu mai laushi sai kawai na farka ײ farka wata keda wuya saina tuna da littafin dake cikin aljihuna.
Wanda na kwanta dashi babban abinda ya bani mamaki kuma ya dauremin Kai babu littafin atare dani haka nata cajin kaina kamar mahaukaci.

Amma baya jikina koda na daga idanuwa na gun table din dake gefena sai naci karo dashi a'ajiye bangon littafin jajawur yake tamkar halshen wuta a yayin da aka daureshi da wani bakin kyalle.

Kallon wannan littafin nake cikin yanayin shakku mai hade da tsoro ta yadda littafin nan yabar jikina ya koma kan table.

•Idan kuna so zanci gaba insha Allah

Ya Allah Ka bamu yawan rai mai albarka, Ya Allah Kasa rayuwarmu tai albarka, Ya Rabb Kabamu jinkirin rayuwar mai amfani,...
24/02/2023

Ya Allah Ka bamu yawan rai mai albarka, Ya Allah Kasa rayuwarmu tai albarka, Ya Rabb Kabamu jinkirin rayuwar mai amfani, Ya Allah Kasa mu gama da duniya lafiya, Ka karbi ranmu cikin imani da Kai, Ka kuma sanya kwanciyar kabarin mu ta zamo ni'ima a garemu, sannan Kai mana sakaiya da gidan Aljannah ranar gobe Qiyama. Allah kayi mana arziki mara yankewa Allah kajikan dukkan magabatanmu, ameen.

Wannan zaben da muke shirin shiga Allah yasa ayi lapiya agama lapiya Allah ya zaba mana mafi alheri. Allah ya karawa kasarmu tsaro da kwanciyyar hankali, ameen.

Barka da juma'a!

23/02/2023

17/11/2022
GWASKA COMIN SOON
25/09/2022

GWASKA COMIN SOON

Barka da sallah
16/07/2022

Barka da sallah

Izzar so teams
06/06/2022

Izzar so teams

Teema yola (RUKAYYA)
12/05/2022

Teema yola (RUKAYYA)

Zarah diamon
05/05/2022

Zarah diamon

Abubakar bashir mai shadda
04/05/2022

Abubakar bashir mai shadda

Mommy gombe
30/04/2022

Mommy gombe

Allah ya karbi ibadun mu, ya inganta rayuwarmu, ya sanyawa kasuwancin mu albarka, ya raya zuri’armu bisa tafarki madaida...
25/04/2022

Allah ya karbi ibadun mu, ya inganta rayuwarmu, ya sanyawa kasuwancin mu albarka, ya raya zuri’armu bisa tafarki madaidaici, ya kawo mana karshen tashin hankalin da kasarmu ke fuskanta, ya kawo bamu shugabanni adalai masu jin kai, ya yafe mana zunubanmu, ya bamu ikon taimakon masu bukata. ya daukaka addininmu, ya kuma sa aljanna ce makomarmu.

Nazir dan hajiya Member of house of Assembly kura local governments
18/04/2022

Nazir dan hajiya

Member of house of Assembly kura local governments

Address

Babura
Jigawa

Telephone

+2348147285809

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Twins hausa media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share