IYA RUWA

IYA RUWA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from IYA RUWA, Media/News Company, Dutse, Jigawa.

24/05/2026
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fitar da jadawalin lokuta da shirye-shiryen ayyuka na zaɓukan shekarar 2027...
20/04/2026

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fitar da jadawalin lokuta da shirye-shiryen ayyuka na zaɓukan shekarar 2027.
Wannan na kunshe ne a cikin jadawalin ayyukan da Sakataren Tsare-tsare na ƙasa na jam’iyyar, Sulaiman Muhammad Argungu ya sanya wa hannu.
Jadawalin ya bayyana, daga cikin sauran abubuwa, lokutan tantance ‘yan takara (screening), sauraron ƙorafe-ƙorafe (appeals), da zaɓen fidda gwani (primaries), tare da umarnin sayar da fom ɗin tsayawa takara da na nuna sha’awa.
Jam’iyyar APC ta sake tabbatar wa ‘ya’yanta, masu ruwa da tsaki da ‘yan Najeriya cewa za ta gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci, wanda zai ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida ta jam’iyyar da kuma bunƙasa manufofinta na ci gaba.
A cewar jadawalin, sayar da fom zai fara daga ranar Asabar, 25 ga Afrilu, kuma zai ƙare ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026.
Jadawalin ya nuna cewa:
Zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gudana tsakanin 15 zuwa 16 ga Mayu
Majalisar Wakilai: 18 ga Mayu
Majalisar Dattawa: 20 ga Mayu
Majalisun Dokokin Jihohi: 21 ga Mayu
Gwamnoni: 23 ga Mayu, 2026
Haka kuma, jadawalin ya nuna cewa sauraron ƙorafe-ƙorafe zai gudana kamar haka:
Shugaban ƙasa: 18 ga Mayu
Majalisar Wakilai: 20 ga Mayu
Majalisar Dattawa: 21 ga Mayu
Majalisun Dokokin Jihohi: 23 ga Mayu
Gwamnoni: 25 ga Mayu, 2026
Dangane da kuɗin fom:
Masu neman takarar shugaban ƙasa za su biya na nuna sha’awa Naira miliyan 30, yayin da fom ɗin tsayawa takara ya kai Naira miliyan 70
Masu neman gwamna: Naira miliyan 10 (nuna sha’awa) da Naira miliyan 40 (fom)
Sanata: Naira miliyan 3 (nuna sha’awa) da Naira miliyan 17 (fom)
Majalisar Wakilai: Naira miliyan 1 (nuna sha’awa) da Naira miliyan 9 (fom)
Majalisun Jihohi: Naira miliyan 1 (nuna sha’awa) da Naira miliyan 15 (fom)
Jam’iyyar ta ƙara da cewa mata, matasa da masu larura za su biya kuɗin fom ɗin nuna sha’awa kawai tare da rabin kuɗin fom ɗin tsayawa takara (50%).

Address

Dutse
Jigawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IYA RUWA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share