17/07/2023
BIKIN KADDAMAR DA SAYAR DA TAKIN ZAMANI!
Mai girma gwabnan Jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya halarci bikin kaddamar da sayar da takin zamani na jihar jigawa wadda aka gababar a harabar hukumar sayar da kayan aikin gona ta jiha.
Tun a wancan satin ne idan ba a manta ba, mai girma gwabnan ya kaddamar da kwamatin rabon takin, wadda shugaban ma'aikata na gudan gwabnatin jihar jigawa shi ne shugaban kwamatin da ke da alhakin sayar da takin zamani Kai tsaye ga manoma a farashi mai ruhusa.
Takin zamanin wadda ake sayar da shi a kan farashin N26,000 a doron Kasuwa; gwabnatin jiha ta saukaka wa manoman wajen sayar da shi a kan N16,000.
Sannan gwabnan ya gargadi jami'an hukumar ta JASCO da kungiyoyin manoma, wajen karkatar da takin ta hanyar da ba ta dace ba ..su tabbatar takin yanke hannun manoma Kai tsaye. Sannan kada a sayar wa da mutum taki sama da buhu biyar. Sannan ya hori jami'an tsaro da su tabbatar da sun sa ido wajen tabbatar da an yi abin da ya kamata wajen sayar da takin.
Taron ya samu halartar mataimakin gwabna, kakakin majalissa, manyan jami'an gwabnati, sakataren gwabnatin jiha, shugaban ma'aikata na gidan gwabnat, 'yan majalissar jiha, shugabannin kananan hukumomi, kungiyoyin manoma, jami'an tsaro da sauran al'umma.
Mallam Garba Al-Hadejawy, FCAI, FIMC
S.A New Media, Jigawa State.