21/09/2025
Jami’ar European-American ta nesanta kanta da digirin girmamawa da aka bai wa mawaki Rarara
Jami’ar da ake kira European-American University ta ce ba ta da hannu a bikin da aka gudanar a Abuja inda aka ce ta bai wa mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, digirin girmamawa.
A ranar Asabar aka shirya bikin a otal ɗin NICON Luxury Hotel da ke Abuja, inda danginsa da abokansa s**a halarta domin taya shi murna.
Sai dai jami’ar ta wallafa sanarwa a shafinta na intanet, tana mai bayyana cewa taron yaudara ne da ba ta amince da shi ba.
Ta ce akwai wani mutum da aka bayyana da sunan Musari Audu Isyaku a matsayin wakilin jami’ar a Arewacin Najeriya, jami'ar ta ce ba shi da wani izini daga wurinta.
Haka kuma ta ƙara da cewa Idris Aliyu, wanda aka gabatar a matsayin mamba a majalisar gudanarwar jami’ar, hallau ba shi da wannan matsayin. Jami’ar ta bayyana cewa ba ta da wata “majalisar gudanarwa,” tare da sanar da cewa ta janye duk wani matsayi da ta taɓa ba shi saboda rawar da ya taka a shirya wanna biki.
Tun da farko dai jami’ar ta raba irin wannan digirin girmamawa ga wasu fitattun ’yan Najeriya, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da kuma Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar Borno, Mustapha Gubio.
Me za ku ce?