AAR Hausa

AAR Hausa Kafar Jaridar AAR Hausa Tana Kawo Muku Labaran Gaskiya Da Nishadi Awa 24/ Kuci Gaba Da Bibiyan Mu.
(16)

YANZU-YANZU: Matasan Arewa sun shirya zanga-zangar lumana kan wulakanta su da ake yi a Najeriya Wata kungiya ta matasa m...
18/10/2025

YANZU-YANZU: Matasan Arewa sun shirya zanga-zangar lumana kan wulakanta su da ake yi a Najeriya

Wata kungiya ta matasa mai suna Matasan Arewa Youth Development Initiative ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ke nuna sakaci da raini ga matasa ta hanyar kin ba su gurbi a cikin mulki.

Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano a ranar Alhamis, shugaban kungiyar na kasa, Abba Muhammad, ya ce kungiyar, wacce ta kunshi matasan Arewa da s**a taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2023, ta kammala shirin fara zanga-zangar lumana da zagayen wayar da kai a jihohin Arewa 19.

Ya ce manufar wannan zanga-zanga ita ce nuna rashin jin dadin yadda gwamnati ta yi watsi da matasa, tare da fadakar da al’umma kan muhimmancin wakilcin matasa da hada su cikin harkokin mulki da ci gaban kasa.

“Mu ne muka yi yakin neman zabe, muka tashi tsaye muka tabbatar da nasara. Amma yanzu kusan shekaru biyu kenan cikin wannan gwamnati, matasan Arewa da s**a tsaya a gaba a lokacin zabe an yi watsi,” in ji Abba.

Ya kara da cewa kungiyar na nuna damuwa da yadda Shugaban kasa da jam’iyyar APC s**a kasa cika alkawuran da s**a dauka ga matasa, musamman wajen muk**ai da tsare-tsaren gwamnati.

“Ba mu neman tallafi ko kyauta,” in ji shi. “Abin da muke nema shi ne a gane muhimmancin matasa, a ba su dama su ba da gudunmawa wajen gina kasa.”

Abba ya bayyana cewa zanga-zangar lumana da zagayen wayar da kai zai fara daga jihar Kano a karshen wannan watan, kuma zai hada da tarukan tattaunawa da jama’a, hulda da kafafen yada labarai, da shirye-shiryen fadakarwa a kauyuka.

A cewar kungiyar, wannan mataki na da nufin ta da wayar da kai da kuma karfafa himmar siyasa a tsakanin matasan Arewa, tare da kira ga gwamnati da ta girmama rawar da matasa s**a taka a lokacin zabe da kuma hada su cikin tafiyar mulki.

DDL Hausa

18/10/2025

Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki

Mutane 7 sun hadu da ajalinsu sak**akon hatsaniya tsakanin ‘yan bindiga da masu hakar ma’adanai a Birnin Gwari ta  jihar...
18/10/2025

Mutane 7 sun hadu da ajalinsu sak**akon hatsaniya tsakanin ‘yan bindiga da masu hakar ma’adanai a Birnin Gwari ta jihar Kaduna

Gwamnatin Ivory Coast ta haramta gangamin siyasa na tsawon watanni biyu a yayin da mako guda ya rage a yi zaben shugaban...
18/10/2025

Gwamnatin Ivory Coast ta haramta gangamin siyasa na tsawon watanni biyu a yayin da mako guda ya rage a yi zaben shugaban kasa

Wasu na ganin gwamnatin ta yi haka ne don hana wasu 'yan adawan kasar neman kuri'a baya ga 'yan takara biyar da aka amincewa shiga takara a zaɓen inji jaridar Punch.

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Ibrahim Shettima, ya t...
18/10/2025

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Ibrahim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa; nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, a wani sabon mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar.



Da yake jawabi, a yayin taron sabunta samar da mak**ashi a Nijeriya (NREIF) ranar Talata a Abuja, Shettima ya ce; zuciyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da ‘yan Nijeriya, sannan kuma yana sane da irin radadin da suke ji.

“Zuciyar shugaban, na matukar rashin jin dadi, dangane da radadin da ‘yan Nijeriya ke fama da shi, amma kuma muna bayar da tabbacin cewa; ana dab da samun saukin warwarewar al’amuran baki-daya.”

Mun samu labarin cewa, Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA), ta shirya taron ne domin neman saka hannun jari, wajen samar da kayayyakin da ake sabuntawa a cikin gida.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da mak**ashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na mak**ashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060.
Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da mak**ashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060. Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin yana bukatar kirkire-kirkire, bayar da gudunmawa a cikin gida da kuma sadaukarwa.

“Wannan shi ne dalilin da yasa taken taron na bana ya kasance a matsayin, Aiwatar da Manufofin Nijeriya na Farko da Gudanar da Ci gaban Abubuwan Cikin Gida da kuma Samar da Mak**ashi, yana da matukar muhimmanci. Kazalika, yunkurinmu na dabarun masana’antu a Nijeriya na kira gare mu da mu dage kan makomar hanyoyin samar da mak**ashi na Afirka a nan gida.”

Ya kara da cewa, a karkashin wannan, an hada sama da dala miliyan 400 na sabbin alkawuran saka hannun jari a bangaren sabunta mak**ashi mai a Nijeriya.

A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce; taron NRIP na 2025, ba wani taro ne da kawai aka shirya ba, sai dan shelanta cewa, Nijeriya a shirye take ta jagoranci sauye-sauyen mak**ashin da ake samu a Afirka.

Taken taron na bana shi ne, ‘Aiwatar da Manufofin Najeriya na Farko’, yana magana ne a kan wani abu mai mai muhimmanci da ya dara masana’antu, wanda ya kunshi jajircewa, kwarewar masana’antu da kuma dorewar tattalin arziki na tsawon lokaci.

“A bangaren samar da wutar lantarki, manufar Najeriya ta farko ta nuna aniyar tabbatar da cewa; zamani na gaba na fasahar samar da mak**ashi mai inganci, tun daga na’urori masu amfani da hasken rana har zuwa na’urorin adana mak**ashin batiri da aka baza a fadin kasar, na alfahari tare da dauke da lakabin, “Wanda aka samar a cikin gida Nijeriya’.”

18/10/2025

Zamu bude Postings namu da

Muhammadur Rasulullah

Jarumar Kennywood Nafisa Abdullahi Na Cigaba Da Shanawarta A Kasar Waje.
17/10/2025

Jarumar Kennywood Nafisa Abdullahi Na Cigaba Da Shanawarta A Kasar Waje.

17/10/2025

Daga nan zuwa Gobe zamu ga mutun miliyan nawa ne zasu kai gaisuwa ga Muhammadur Rasulullah (S.A.W.)

YANZU-YANZU: Madugun Darikar Kwakwasiyya Dr Rabi'u Kwankwaso ya yi ganawar sirri da Janar Babangida Jagoran Jam’iyyar NN...
17/10/2025

YANZU-YANZU: Madugun Darikar Kwakwasiyya Dr Rabi'u Kwankwaso ya yi ganawar sirri da Janar Babangida

Jagoran Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi wata ganawa da tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), a gidansa dake Hilltop, Minna, Jihar Neja, a yau Jumma’a.

A yayin ziyarar, Sanata Kwankwaso ya samu rakiyar Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dakta Ahmed Ajuji, inda s**a gudanar da ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasar, k**ar yadda mai taimakawa Kwankwaso a bangaren kafafen yada labarai, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas Ya Angwance Da Tsaleliyar Sabuwar Amaryarsa A Ya...
17/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas Ya Angwance Da Tsaleliyar Sabuwar Amaryarsa A Yau Juma'a

Wane fata kuke yi musu ?

Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, ya yi alkawarin t...
17/10/2025

Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, ya yi alkawarin tabbatar da aniyar ganin ana tafiyar da ayyuka a daidai a Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.

Dantsoho wanda kuma shi ne, Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Kula da Harkar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Afrika ta Yamma wato IAPH ya sanar da cewa, hakan zai taimaka, wajen magance kalubalen da Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a yankin, ke fuskanta.

Kazalika, ya ce, NPA na ci gaba da yin kokari wajen sama da saukin wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wanda hakan ya sanya, har manyan Jiregen Ruwa s**a fara shigo da manyan Kwantainoni zuwa cikin Tashoshin.

Dantawaye ya zama sabon kwamishinan 'yan sandan Abuja, babban birnin NijeriyaCP Dantawaye Miller ya k**a aiki a matsayin...
17/10/2025

Dantawaye ya zama sabon kwamishinan 'yan sandan Abuja, babban birnin Nijeriya

CP Dantawaye Miller ya k**a aiki a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na 34 da zai jagoranci rundunar 'yan sandan babban birnin Nijeriya, Abuja.

Miller ya karɓi ragamar shugabancin rundunar ne daga hannun CP Ajao Adewale, wanda sufeto janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya tura zuwa wani sabon muhimmin aiki.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AAR Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share