Jigawa Online Media

Jigawa Online Media MEDIA/NEWS company

07/10/2025

Kome Yake Faruwa Ne A Sakatariyar Mulki Ta Karamar Hukumar Birninkudu?

Ku Bamu Labarin Abin Da Kuka Sani.

Sheik Pantami Ya Jagoranci Yaye Matasa 'Yan Ajin Farko Da Ya Koyawa Sana'ar Gyaran Waya Da Amfani Da Fasahar AI Da Saunr...
06/10/2025

Sheik Pantami Ya Jagoranci Yaye Matasa 'Yan Ajin Farko Da Ya Koyawa Sana'ar Gyaran Waya Da Amfani Da Fasahar AI Da Saunransu

A yau Litinin Sheikh Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya) ya jagoranci bikin yaye matasa 250 Batch na farko 'yan asalin jihar Gombe da ya koyawa sana'ar gyaran waya da amfani da fasahar AI da Cyber Security tare da basu kayan aikin gyaran waya na zamani da takaddar shaidar karbar horo na musamman.

Muna Addu'ar Allah ya sanya Albarka.

"A koya maka yadda ake kamun kifi, yafi a kamo kifin a baka shi a hannu".

YANZU-YANZU: Sheikh Farfesa Isa Pantami Ya Kai Ziyarar Karfafa Gwiwa Ga Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD A Jihar GombeTsoh...
06/10/2025

YANZU-YANZU: Sheikh Farfesa Isa Pantami Ya Kai Ziyarar Karfafa Gwiwa Ga Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD A Jihar Gombe

Tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya, Sheikh Professor Isa Ali Ibrahim Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya), ya kai ziyara ta musamman zuwa ofishin kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, da ke cikin garin Gombe, domin karfafa gwiwa da ba da shawarwari ga ma’aikata da shugabannin kamfanin kan ci gaba da gudanar da sana’arsu cikin natsuwa da inganci.

A yayin ziyarar, Sheikh Pantami ya yaba da kokarin kamfanin wajen bunkasa harkokin fasahar sadarwa (ICT) a yankin Arewa, inda ya jaddada muhimmancin sabbin kirkire-kirkire, gaskiya, da aminci a cikin harkar kasuwanci.

Shugaban kamfanin, Abba Sani Pantami ya bayyana cewa sun karɓi ziyarar da farin ciki da girmamawa matuka, yana mai cewa:

“Mun ji dadi sosai marar misaltuwa da wannan ziyara. Sheikh Professor Isa Ali Pantami ya karrama mu ya mutuntamu fiye da yadda muka zata. Ziyararsa ta kara mana kwarin gwiwa sosai.”

A wannan ziyara, Sheikh Pantami yana tare da Alhaji Abubakar Walama (Sarkin Malaman Gombe), Professor Abubakar Muhammad Bello (tsohon Manajan Darakta, Galaxy Backbone Limited), Mallam Muhammad Yahaya Tambura (tsohon Darakta-Janar na ZICTDA), Alhaji Jamilu Jamo, da kuma sauran manyan ‘yan tawaga da s**a raka shi.

Ziyarar ta kasance wata dama ta musamman da ta karfafa zumunci da hadin kai tsakanin manyan masana na fannin ICT da kamfanonin fasaha na cikin gida, musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Daga Zamani TV

Wallahi Na Fi Karfin Na Yi Mukabala Da Sheik Lawal Triumph, Kuma Da A Ce Ni Zan Yi Mukabala Da Shi Minti Biyar Ya Yi Yaw...
06/10/2025

Wallahi Na Fi Karfin Na Yi Mukabala Da Sheik Lawal Triumph, Kuma Da A Ce Ni Zan Yi Mukabala Da Shi Minti Biyar Ya Yi Yawa Na Gama Da Shi, Cewar Malam Abdulfatahi Sani Attijjaniy

YANZU-YANZU: Sevilla Ta Ragargaji Barcelona Da Ci 4-1
05/10/2025

YANZU-YANZU: Sevilla Ta Ragargaji Barcelona Da Ci 4-1

YANZU-YANZU: Kwamitin Shura ya bukaci Malaman Dake Wajen Kano Dama Waɗan da ke Kano Din da su dakata da ci gaba da tatta...
05/10/2025

YANZU-YANZU: Kwamitin Shura ya bukaci Malaman Dake Wajen Kano Dama Waɗan da ke Kano Din da su dakata da ci gaba da tattaunawa kan batun da ake na tuhumar Malam Lawan Trium.

Kungiyar Bola Tinubu Renewed Hope Sensitisation 2027 ta gudanar da taro a KanoKungiyar Bola Tinubu Renewed Hope Sensitis...
05/10/2025

Kungiyar Bola Tinubu Renewed Hope Sensitisation 2027 ta gudanar da taro a Kano

Kungiyar Bola Tinubu Renewed Hope Sensitisation 2027 ta gudanar da taro a birnin Kano domin ci gaba da wayar da kan jama’a kan kyawawan manufofin Shugaban Ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu.

Taron, wanda ake gudanarwa a yanzu a City King Hotel, Kano, ya tattaro manyan jiga-jigan kungiya da magoya baya daga sassa daban-daban na jihar.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisar dokokin jihar Jigawa mai wakiltar karamar hukumar Jahun, Hon. Alhaji Idris Garba Kareka.

An bayyana cewa, manufar taron ita ce ƙarfafa goyon bayan jama’a ga shirin gwamnatin Tarayya na Renewed Hope Agenda, tare da yada sakonnin ci gaba da cigaba da tafiya tare da Shugaban ƙasa.

Wata Gidauniya Ta Gina Rijiyar Sadaukarwa Ga Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari A AdamawaDaga Muhammad Kwair...
04/10/2025

Wata Gidauniya Ta Gina Rijiyar Sadaukarwa Ga Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari A Adamawa

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Wata gidauniya ta kammala aikin gina rijiyar burtsatse a ƙauyen Jamtari da ke ƙaramar hukumar Mayo-Belwa a jihar Adamawa, a matsayin sadaukarwa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

An gina rijiyar ne domin amfanar da al’ummar yankin da dogon lokaci ke fama da karancin ruwan sha. Gidauniyar ta bayyana cewa aikin ya kasance wata hanya ta girmamawa da tunawa da rawar da Buhari ya taka wajen jagorantar Najeriya.

Sun kuma yi fatan Allah ya karɓi sadaukarwar, ya gafarta masa, ya sanya kabarinsa cikin rahama.

Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira da A Sasanta Rikicin Kano Cikin Lumana, Ya Yabi DSS Kan Rawar da Ta TakaShugaban Jama’atu Iza...
01/10/2025

Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira da A Sasanta Rikicin Kano Cikin Lumana, Ya Yabi DSS Kan Rawar da Ta Taka

Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta tarayyar Nigeria, Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau , ya yi kira da a kwantar da hankali da nuna haƙuri wajen tafiyar da rikicin addini da ke ci gaba a Kano, inda ya gargadi mutane da su guji amfani da lamarin don haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al’ummar Musulmi.

A lokacin da yake gabatar da wa’azi a makon jiya wajen taron ƙungiyar ‘Federation of Ahlusunnah Organization in Nigeria’ (FAFSON) da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, Sheikh Bala Lau ya yaba da hangen nesa da kwarewar Darakta Janar na Hukumar Tsaro na Farin kaya (DSS), Mista Tosin Ajayi, wajen tabbatar da lamarin zuwa hanyar zaman lafiya ba tare da zuwa kotu ba.

“Ina yabawa shugabancin DSS bisa tabbatar da cewa an tafiyar da wannan al’amari cikin hikima da lumana. Kai shi kotu zai iya tada jijiyoyin wuya kuma ya tsawaita rikicin. Abin da al’ummar Musulmi ke buƙata a yanzu shi ne hikima, haƙuri da haɗin kai,” in ji shi.

Malam ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ci gaba da zama tsaka-tsaki, yana jaddada cewa shiga gefen kowane ɓangare na iya ƙara rarrabuwar kai da lalata zaman lafiya a jihar.

“A irin wannan lokaci, bai kamata gwamnati ta nuna tana goyon bayan ɓangare guda ba. Adalci da gaskiya suna buƙatar a tsaya a tsaka-tsaki. Aikinmu a matsayin shugabanni shi ne kiyaye zaman lafiya, ba ƙara wa rikici wuta ba,” in ji Sheikh Bala Lau.

Jawabansa sun biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar tare da mayar da martani ga Majalisar Shura ta Jihar Kano kan zargin kalaman batanci da ake alakanta Shi da Sheikh Lawan Shuaibu Abubakar Triumph. Majalisar ta bayyana cewa za ta saurari masu ƙorafi da kuma malamin kafin ta ba da wani shawari ga gwamnati.

Sai dai Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Musulmi da kada su bari zarge-zargen su rinjaye su, yana gargadi cewa irin waɗannan muhawarori idan ba a kula ba za su iya bata sunaye kuma su kau da hankali daga babbar manufar ƙarfafa addini.

“Kano ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da s**a fi zaman lafiya a Arewa maso Yamma. Bai kamata mu bari rikice-rikicen su lalata wannan tarihi ba. Mu kiyaye harsunanmu, mu guji zagin juna, mu kuma yi aiki tare domin bunƙasar Musulunci da al’ummarmu,” in ji shi.

Taron Ibadan ya tattaro manyan malamai da masu ruwa da tsaki daga sassan Najeriya domin tattaunawa kan haɗin kai, da’awa da rawar jagorancin addini wajen tabbatar da zaman lafiya.

Jibwis Nigeria

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa...
01/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.

Bayan Fitowa Daga Studio Shugaban ƙaramar Hukumar Birnin-Kudu Ya Rabawa Wasu Daga Cikin Al'ummar Da Yake Shugabanta Many...
01/10/2025

Bayan Fitowa Daga Studio Shugaban ƙaramar Hukumar Birnin-Kudu Ya Rabawa Wasu Daga Cikin Al'ummar Da Yake Shugabanta Manyan Riguna...

Abubakar Shehu Dokoki ✍️

A gobe Laraba da safe Tinubu zai yi wa ‘yan kasa jawabi, kan ranar samun 'yan cin kai.
30/09/2025

A gobe Laraba da safe Tinubu zai yi wa ‘yan kasa jawabi, kan ranar samun 'yan cin kai.

Address

Takur Site Layin Kosai Opp Godiya Miyatti Market, Dutse
Jigawa

Telephone

+2347062795419

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jigawa Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share