
03/08/2025
SERAP TA BAIWA GWAMNA NEJA WA'ADIN SA'O'I 48 YA JANYE UMARNIN RUFE WANI GIDAN REDIYO A JIHAR
Kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da gaskiya ta SERAP ta bai wa Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, wa’adin sa’o’i 48 domin ya janye matakin rufe tashar rediyon Badeggi FM, mai zaman kansa dake Minna, babban birnin jihar.
A cikin wata budaddiyar wasika da ta wallafa a jiya asabat, wacce Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sa wa hannu, kungiyar ta bayyana matakin gwamnatin jihar a matsayin danniya da rashin bin doka, tana mai bukatar a dawo da lasisin tashar tare da janye barazanar rushe ginin ta.
SERAP ta kuma nemi Gwamna Bago da ya daina kai hare-hare kan mamallakin tashar, Shuaibu Badeggi, da sauran ma’aikatanta, tare da bayar da tabbacin lafiyar su da ‘yancinsu a fili.
Wannan martani na SERAP na zuwa ne bayan Gwamna Bago ya bayar da umarnin rufe tashar a ranar Juma’a, tare da soke lasisinta, da kuma umurta Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da ya binciki bayanan mamallakin tashar.