14/12/2024
Imamu shafi’i yace mutun biyar ne masu hankali a wannan duniyar
(1) mai hankali na farko shi ne wanda ya nemi yardar Allah kafin haduwa da Allah.
(2) mai hankali na biyu shi ne wanda ya gina kabarin sa kafin ya shi ga kabarin.
(3) mai hankali na uku shi ne wanda yabar duniya kafin duniyar tabarshi.
(4) mai hankali na hudu shi ne wanda yayi wa kansa hisabi kafin ranar da za’a tsayar da shi A yi masa hisabi.
(5) mai hankali na biyar shi ne wanda yake yin sallah a cikin jam’i kafin ranar da mutane za su yi jam’i su salla ce shi.
Allah yasa mu rabu da wannan duniyar lafiya ba tare da munyi nadamar rayuwa A cikinta ba saboda mutuncin Annabi Muhammad saw