29/07/2025
"ADC Za Ta Mutu Nan Bada Jimawa Ba, Obi Zai Koma PDP" — Ali Modu Sheriff
Daga Umar Alhaji Audu
Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa sabuwar jam’iyyar hadaka da aka kafa, wato African Democratic Congress (ADC), ba za ta daɗe ba za ta rushe.
A cewarsa, jam’iyyar ADC da aka ƙaddamar kwanan nan tare da haɗin gwiwar wasu manyan ’yan adawa ciki har da tsofaffin gwamnoni, ministoci da kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ba za su iya fuskantar ƙalubalen karɓar mulki daga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyya mai mulki ta APC a zaben shekarar 2027 ba.
Ali Modu Sheriff ya kuma nuna tabbacin cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a 2023, zai dawo cikin PDP nan ba da jimawa ba.
Abdulaziz Bali