29/04/2025
KOMAI NAKA ZAIZO ƘARSHE:😭😢💔
-
"Kullum kana rayuwa tamkar bazaka mutu ba, kana tunanin kamar abinda ka tara bazai taɓa ƙarewa ba, ji kake kamar zaka dauwama ne acikin wannan duniyar, a tunaninka mulkinka da ikonka za suyi maka shamaki da mutuwa, domin a tunanin ka wai bazasu rabu da kai ba"
-
"Wannan shine ƙarshen komai naka, dukiyarka, lafiyarka, rayuwarka, matsayinka, mulkinka, ikonka, kyawunka, ilminka, duk abinda ka mallaka a wannan duniyar, to yau ce ranar tafiya ka barshi, Ya Allah kasa muje a sa'a"
-
"Za kaje ka haɗu da ubangijinka Allah, daga kai sai shi, ga kuma aikin ka a gefe guda yana jiran ayi maka hisabi domin kai da kanka ka tabbatar da inace makomarka"
-
Ya Allah kasa mu zamto daga cikin ahlin aljannah maɗaukakiya.
Allah ka Gafartawa Al'ummar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi wasallam Ameen
Domin Samun Fadakarwa Tunatarwa da sauran karatun Addini
Auwal Muhammad follow