23/07/2025
Wata mata suna cikin karin kumallo tare da mijinta, sai ta kalli tagar da ke kallon waje, ta ga makwabciyarta tana shanyar kayan wanki. Sai ta ce wa mijinta:
"Ka duba wani irin wanki, sam sam bai fita ba. Wannan matar ba ta iya wanki sosai ba."
Mijinta ya kalli tagar amma bai ce komai ba, ya yi shiru.
Kullum idan makwabciyarsu ta shanyar wanki, sai matar nan ta maimaita wannan maganar ga mijinta.
Wata rana, sai ta duba tagani sai ta ce wa mijinta:
"Subhanallah! Kalli wankin ta na yau ya fita sosai kuma yayi kyau."
Sai mijinta ya ce mata:
"Abunda ya faru shi ne yau na farka da wuri sai na goge tagar gidanmu da kura da datti s**a taru s**a yi yawa a kai."
KU FITO MANA DA DARUSSAN DA KUKA DAUKA DAGA CIKIN WANNAN LABARIN.