Amana News

Amana News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Amana News, Media/News Company, Jos.

AMANA NEWS is a trusted digital news platform dedicated to delivering accurate, balanced, and timely information on politics, business, education, health, sports, and human-interest stories.

IYALAN MALAM NASIR EL-RUFAI SUN MOTSAIyalan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun bawa Babban Ministan Ts...
07/09/2026

IYALAN MALAM NASIR EL-RUFAI SUN MOTSA

Iyalan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun bawa Babban Ministan Tsaro Christopher Musa wa'adin kwanaki 7 a kan ya janye kalamansa na sharri akan Malam, idan ba haka ba zasu dau matakin shari'ah a kansa

Wannan mataki da iyalan Malam Nasir El-Rufai s**a dauka yayi daidai, kuma sun kyauta

Muna rokon Allah Ya kubutar da Malam Nasir daga sharrin makiya

Datti Assalafiy

DAGASKE NE SHEIKH JINGIR YANA CIKIN TAWAGAR YAƘIN NEMAN ZAƁEN TINUBU?Tun bayan sakin kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnati...
07/09/2026

DAGASKE NE SHEIKH JINGIR YANA CIKIN TAWAGAR YAƘIN NEMAN ZAƁEN TINUBU?

Tun bayan sakin kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnatin APC ta shugaban ƙasa Tinubu a kafafen watsa labarai da sadarwa, wasu daga cikin ma'abota shafukan suke zargin sunan Sheikh Sani Yahaya Jingir ya fito a ciki.

To sai dai binciken Amana News ya tabbatar da cewa sunan da ya bayyana a jikin takardar sunayen, wato SANI YAHAYA na wani matashi ne mai suna YAHAYA SANI ABUBAKAR ɗan jihar Kaduna.

Asalin mai sunan ya karanta MASS COMMUNICATION ne a jami'ar Bayero dake Kano, wanda ya kammala a shekarar 2023. Tun kafin yanzu, matashin ya kasance dan jam'iyar APC.

Kafin yanzu, Asalin mai sunan, wato YAHAYA SANI ABUBAKAR, ya taɓa yin irin wannan aiki a baya, kamar dai yadda kuke gani a jikin hoto.

Da Wannan ne Amana News ta ke kira ga al'umma da su guji yaɗa labarun ƙarya don neman suna.

JIBHAN NHQ JOS Jibwis.nat HQ Jos Kumbotso Branch Kano State ゚viralシfypシ゚ SURAJ JOURNALISt

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!!Allah Ya yi wa Zainab Diamond wato Talatuwa - Maman Bintalo a shirin mu na Labarina...
07/09/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

Allah Ya yi wa Zainab Diamond wato Talatuwa - Maman Bintalo a shirin mu na Labarina rasuwa.

Mu na rokon addu'ar fatan samun rahama gare ta daga gare ku.

Allah Ya jikan ta gafara. Ya sa aljanna makoma gare ta da sauran musulmi baki ɗaya da su ka rasu.

- Ahmad Nagudu
A madadin Saira Movies

📸: Nagudu TV

゚viralシ

BAUCHI DETECTIVES ARREST 20-YEAR-OLD MAN FOR ALLEGED DEFILEMENT OF A MINOR AND ROBBERY OF TWO PHONES IN DARAZOThe Bauchi...
07/09/2026

BAUCHI DETECTIVES ARREST 20-YEAR-OLD MAN FOR ALLEGED DEFILEMENT OF A MINOR AND ROBBERY OF TWO PHONES IN DARAZO

The Bauchi State Police Command has arrested a 20-year-old man for allegedly luring a 7-year-old girl into an uncompleted building, having unlawful carnal knowledge of her and dispossessing her of two mobile phones in Darazo.

The arrest followed a complaint lodged on 6th September, 2026 at about 1630hrs by a 37-years-old father, a resident Kari village via Darazo, who reported alongside his 7-years-old daughter, that on the same date at about 0800hrs, the victim was on her way to a neighbouring house with two Android phones of the same make, Techno A31, when one Isiyaku Usman 'm', 20-years-old, of the same address, lured her into a nearby uncompleted building, robbed her of the phones and forcefully had sexual in*******se with her.

Upon receipt of the complaint, detectives swiftly swung into action and arrested the suspect in possession of the stolen phones. Both the victim and the suspect were immediately conveyed to Darazo General Hospital for medical examination, while their statements were recorded. The suspect voluntarily confessed to the commission of the offences and is currently in detention, undergoing further preliminary investigation.

While condemning the senseless, heinous act, CP Sani-Omolori Aliyu, mni psc(+), directed that the case be transferred to the Gender Laboratory of the State Criminal Investigation Department, Bauchi, for discreet investigation, after which the suspect will be charged to court.

In a statement issued Monday, September 7th by SP Nafiu Habib, ANIPR, FFIS, Police Public Relations Officer in the state said the Command reiterates its zero tolerance for sexual and gender-based violence and urges parents and guardians to remain vigilant over the movement and safety of their children, while assuring the public of its commitment to ensuring justice is served.

゚viralシfypシ゚

KUSAN CUTAR  DIPHTHERIA JIBHAN TA GABATAR DA BINCIKE DA HUJJOJI AKAN CUTAR DIPHTHERIA. 1. GANE ALAMOMI • HANA YAƊUWAR CU...
07/09/2026

KUSAN CUTAR DIPHTHERIA

JIBHAN TA GABATAR DA BINCIKE DA HUJJOJI AKAN CUTAR DIPHTHERIA.

1. GANE ALAMOMI • HANA YAƊUWAR CUTAR • CETO RAI.

Jibwis Health Association of Nigeria (JIBHAN) na wayar da kan al’umma game da cutar Diphtheria, wata cuta ce mai hatsari wadda ke iya jefa rayuwa cikin haɗari idan ba a gano ta da wuri ba kuma idan ba a samu kulawar lafiya cikin gaggawa ba.

1. Muhimman Alamomin Cutar daya kamata a kula dasu:

• Zazzabi.
• Ciwon makogwaro.
• Tari.
• Majina ko toshewar hanci.
• Wahalar haɗiye abinci ko ruwa.
• Wahalar numfashi.
• Kumburin wuya.
• Samuwar wani kauri mai launin toka ko fari a makogwaro ko hanci.
• Rauni da kuma ƙara tsanantar rashin lafiya.

Duk wanda ya nuna irin waɗannan alamomi yayi maza maza ya nemi kulawar ma’aikatan lafiya cikin gaggawa, ba tare da jira cutar ta tsananta ba.

2. Ta Yaya Cutar Ke Yaɗuwa?

Diphtheria na iya yaɗuwa ta hanyar:

• Tari ko atishawa daga mai ɗauke da cutar.
• Kusanci da wanda ya kamu da cutar.
• Taɓa majina ko sauran ruwan jiki na mai cutar.
• Saduwa da raunukan fata masu ɗauke da cutar.
• Amfani da wasu abubuwan sirri da mai cutar ya yi amfani da su.

3. Hanyoyin Rigakafi
Domin kare kai da al’umma daga cutar Diphtheria:

• A tabbatar an yi allurar rigakafin Diphtheria yadda ya kamata bisa tsarin rigakafin da ma’aikatan lafiya s**a tanadar.

• A riƙa wanke hannu akai-akai da ruwa da sabulu.

• A rufe baki da hanci yayin tari ko atishawa.

• A guji kusanci da wanda ake zargin yana da cutar.

• Idan alamomin cutar sun bayyana, a garzaya cibiyar lafiya.

• A bi shawarwarin ƙwararrun ma’aikatan lafiya da hukumomin lafiya.

• Kada a yi ƙoƙarin cire farin ko ruwan toka da ke makogwaro da hannu ko wani abu.

4. Me Ya Sa Gano Cutar Da Wuri Yake Da Muhimmanci?

Diphtheria na iya haifar da matsaloli masu tsanani, ciki har da matsalar numfashi da kuma lalacewar zuciya ko jijiyoyi. Saboda haka, gano alamomi da wuri, neman magani cikin gaggawa da kuma rigakafi na da matuƙar muhimmanci wajen ceton rayuka.

Saƙon JIBHAN Ga Al’umma
Rigakafi da wayar da kai na daga cikin mafi muhimmancin hanyoyin kare yara, iyalai da al’umma daga cututtuka masu yaɗuwa.

Mu kasance masu lura da alamomi, mu tabbatar da rigakafi, mu kiyaye tsafta, kuma mu nemi kulawar lafiya cikin gaggawa idan alamun cutar sun bayyana.

KUTUNA:

GANE ALAMOMI • HANA YAƊUWA • NEMI MAGANI DA WURI • CETO RAI

Signed:
Muhammad Abdulrahman Adam
JIBHAN Vice National Secretary.

JIBHAN NHQ JOS

KUSAN BABU WANDA YA TSIRADaga Datti Assalafiy Barayin daji sun harbe Malam Nasiru Gusau Marafa wanda shine Bursar na jam...
07/09/2026

KUSAN BABU WANDA YA TSIRA

Daga Datti Assalafiy

Barayin daji sun harbe Malam Nasiru Gusau Marafa wanda shine Bursar na jami'ar National Open University of Nigeria (NOUN)

Jami'ar NOUN ta tabbatar da mutuwarsa, tace bisa bayanan da Jami’ar ta samu, an harbe Malam Nasiru Gusau Marafa yayin da yake dawowa daga garin Gusau

Malam Nasiru Gusau Marafa ya kasance ma’aikacin jami'a mai kwazo, jajircewa da sadaukarwa wajen yi wa Jami’ar hidima, an nada shi Bursar na National Open University of Nigeria a watan Satumba 2022

Rayuwarsa ta kare a hannun wadanda basu fi karfin a yake su ba, dadin abin kowa zai mutu, kuma za'a tashemu a yiwa kowa hisabi

Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi.

゚viralシfypシ゚

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta fara babban atisaye da horon ƙwarewa ga jami’anta da s**a fito daga kananan hukumomi 2...
06/09/2026

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta fara babban atisaye da horon ƙwarewa ga jami’anta da s**a fito daga kananan hukumomi 27 na jihar da Hedikwatarta.

Arewa Updates ta rawaito cewa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, Dauda Muhammad Hadejia, ne ya bayyana hakan.

Dauda Hadejia ya ce an fara horon ne a ranar Asabar 5 ga Satumba, 2026, a sansanin NYSC da ke Fanisau a birnin Dutse, inda zai ɗauki tsawon mako guda.

Ya bayyana cewa, masu horas da jami’an sun tantance mahalarta bayan isarsu sansanin kafin yi musu rajista bisa kananan hukumomin da s**a fito, tare da ba su katin shaidar rajista da sauran kayan horo.

Hukumar ta bayyana cewa, horon na da nufin ƙara wa jami’anta ƙwarewa, ƙarfafa tarbiyya da ɗa’a, inganta fahimtar ayyukan Hisbah da haɗin kai tsakanin ma’aikata.

06/09/2026

JOS GIDAN NISHAƊI

Yadda wani matashi yake nishaɗantuwa a gurin biki a garin Jos.

゚viralシfypシ゚

Hotunan yadda akayi waazin kasa da kasa a jimhuriyar Niger yadda wakilan sheikh Sani Yahaya Jingir a karkashin jagoranci...
06/09/2026

Hotunan yadda akayi waazin kasa da kasa a jimhuriyar Niger yadda wakilan sheikh Sani Yahaya Jingir a karkashin jagorancin sheikh Dalhat Abubakar Abdullahi Kantana.

Bayan gabatar da waazin dare a yau an ci gaba da waazin Kankarew , yadda aka sami halatar maigirma gwamnan jihar Tahoe Colonel-Major Souleymane Amadou Moussa.

Da fatan Allah ya saka da Alkhairi ya kara daukaka.

JIBHAN NHQ JOS Jibwis.nat HQ Jos Kumbotso Branch Kano State

TINUBU YA BUKACI SHUGABANNI SU FIFITA MURADUN AL’UMMA A ƘASAR NANShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a samu sh...
06/09/2026

TINUBU YA BUKACI SHUGABANNI SU FIFITA MURADUN AL’UMMA A ƘASAR NAN

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a samu shugabanni da ’yan kasa masu kishin kasa, wadanda za su fifita muradun jama’a da ci gaban kasa a kan son kai da neman biyan bukatun kansu.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a yayin wani taron addu’ar godiya da aka gudanar a majami'ar St. Monica Cathedral na LCCN da ke Jimeta a Yola, domin bikin cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dakta Boss Mustapha.

Shugaban, wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume ya wakilta, ya bukaci jami’an gwamnati da sauran ’yan kasa su mayar da hidimar jama’a da kare muradun kasa a matsayin ginshikin ayyukansu.

Ya ce Najeriya na bukatar shugabanni da za su duba abin da ya wuce samun ci gaban kansu, tare da sadaukar da kansu wajen yi wa al’umma hidima da tabbatar da ci gaban kasa.

A nasa bangaren, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana Boss Mustapha a matsayin abin koyi wajen gaskiya da rikon amana a hidimar gwamnati.

Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa a yankin tsakiyar Najeriya da su kara hada kai.

Shi ma Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda mataimakinsa Farfesa Kaletapwa George Farauta ya wakilta, ya yaba da gudunmawar Boss Mustapha wajen gina kasa da kuma jajircewarsa wajen yi wa Najeriya hidima.

Taron ya samu halartar shugabannin siyasa, jami’an gwamnati, ’yan uwa da abokan arziki da dai sauran su.

゚viralシ

Address

Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amana News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share