07/01/2025
Don jin daɗin masoya kaɗai!
Gargaɗi: Idan kai ba ma'abocin wannan harkar bane, ka wuce, ka barwa masu abin kayan su.
Ai Shehu Radhiyallahu Ta'ala Anhu shi ne RUHUL-ƘUDSI (Ruhin Tsarki). Dukkan kaunu cikin sa suke samun madadin Ilahiyya.
Su Shehu Mallam Tijani Radhiyallahu Ta'ala Anhum da kaji suna zantukan wuce hankali akan sa, ka zata haka kawai ne? Ai maye gaskiya ne, kuma ba'a taɓa yin wanda yasha kayan maye ya bugu bai yi maye ba. Ire-iren abubuwan da su Shehu Mallam Tijani Radhiyallahu Ta'ala Anhum s**a ɗanɗano na soyayyar Shehu, baza su taɓa iya tsallakewa ba tare da sun yi wannan mayen ba. Allah na tuba zauna-gari-banza, tataccen ɗan duniya ma yayi maye akan kuɗi ko mulki ballantana kuma na Allah akan kayan Allah?
Ita halarar Shehu Radhiyallahu Ta'ala Anhu, halara ce ta zallar soyayya. Shi yasa take a ƙarshe kuma a farko. Itace tayi Ihaɗa, ta tattaro sauran Halarorin ta zamar da su ɗaya. A cikin ta akwai Jalala da Jamala, Fana'i da Baƙa'i. Idan ka same ta, ka samu Tajalli, Tahalli da Takhalli. Wannan Halarar itace "Majma'ush-Shu'uni" da kaji ana faɗa. Komai na sirrin Ilahiyya, Muhammadiyya da Ahmadiyya yana cikin ta, idan ka same ta ka samu komai.
Mawaƙi yana cewa: "Ni buri na in so ka, ba in gane ka ba, domin duk mai gani bazai iya gane ka ba." Don haka ba Halara bace ta bincike ko sanin sirri, Da'ira ce ta zallar Soyayya. Ayi Soyayya, ayi Hidima, ayi Wuridi. Kada ayi Da'awa. A nufi Ma'abocin halarar, kada a gayyara shi da komai.
Idan kaji mutum ya ce maka adinga kamewa wajen yin zance, gaskiya ya faɗa, kada ka zarge shi. Haka wanda kaji yana ɓarin zance, shi ma ba aikin sa bane. Haka soyayya take. Tamkar kofi ne adinga zuba masa ruwa, idan ya cika babu abinda zai hana shi zuba.
- Tijjaniyyatoptv