Hikima multimedia tv LTD

Hikima multimedia tv LTD Hikima Multimedia TV LTD

Your Trusted Source for Breaking News in English & Hausa. Stay

Breaking News | Politics | Security | Business | Entertainment

Sahihan labarai cikin Hausa da Turanci — cikin sauri, sahihanci da amana.

DA DUMI-DUMINSA: ZIYARA TARE DA TALLAFIN ₦500,000JOS: Ɗan takarar Majalisar Tarayya a jam’iyyar APC mai wakiltar Bassa/J...
26/08/2026

DA DUMI-DUMINSA: ZIYARA TARE DA TALLAFIN ₦500,000

JOS: Ɗan takarar Majalisar Tarayya a jam’iyyar APC mai wakiltar Bassa/Jos North, Hon. Sadeeq Plaza, ya ziyarci ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood, Malam Tanimu Akawu, da ke kwance a Asibitin JUTH sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

A yayin ziyarar, Hon. Sadeeq Plaza ya tallafa masa da kuɗi Naira dubu dari biyar (₦500,000) domin taimaka masa wajen biyan kuɗaɗen jinya.

Muna roƙon Allah Ya saka masa da alheri, Ya kuma bai wa Malam Tanimu Akawu cikakkiyar lafiya.

DA DUMI-DUMINSAJOS: Sarakuna, ’Yan Kasuwa, ’Yan Siyasa, Attajirai, Shehunai da Malamai Sun Halarci Bikin Maulidin Annabi...
25/08/2026

DA DUMI-DUMINSA

JOS: Sarakuna, ’Yan Kasuwa, ’Yan Siyasa, Attajirai, Shehunai da Malamai Sun Halarci Bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW)

Dubban Musulmai ne s**a halarci bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a birnin Jos, Jihar Plateau.

Taron ya samu halartar sarakuna, ’yan kasuwa, ’yan siyasa, attajirai, shehunai da malamai daga sassa daban-daban.

24/08/2026

DA DUMI-DUMINSA: KABIRU MASARI YA BAYYANA ANİYARSA TA BA ƘUNGIYAR IZALA ₦300M

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Masari, ya bayyana aniyarsa ta bai wa Ƙungiyar Izala tallafin ₦300 miliyan.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi, inda ya yi magana kan tallafin da yake shirin bai wa ƙungiyar.

Ku kalli cikakken bidiyon domin jin abin da Kabiru Masari ya faɗa.

24/08/2026

DA DUMI-DUMINSA: Sheikh Jingir Ya Yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana ra’ayinsa kan wasu matakai da manufofin gwamnatin shugaban.

23/08/2026

DA DUMI-DUMINSA: AN HANGO HON. DR. ADAMU ALIYU TARE DA GWAMNAN KANO

An hango Hon. Dr. Adamu Aliyu tare da Gwamnan Jihar Kano a wani muhimmin taro da ya gudana.

Haɗuwarsu ta jawo hankalin jama’a, inda ake jiran ƙarin bayani kan dalilin wannan ganawa.

DA DUMI-DUMINSAJOS: Ƙungiyar Izala Ta Gudanar da Taron Ƙara Wa Juna Sani Kan Kimiyyar Siyasa da Zamantakewar Al’ummaƘung...
23/08/2026

DA DUMI-DUMINSA

JOS: Ƙungiyar Izala Ta Gudanar da Taron Ƙara Wa Juna Sani Kan Kimiyyar Siyasa da Zamantakewar Al’umma

Ƙungiyar Izala ta gudanar da wani taron ƙara wa juna sani da ya mayar da hankali kan sha’anin kimiyyar siyasa da kuma zamantakewar al’umma a yau.

DA DUMI-DUMINSA:Hon. Abdulkadir Hassan (SLA) ya miƙa saƙon godiya ga mahalarta da masu goyon bayan gasar SLA Renewed Hop...
22/08/2026

DA DUMI-DUMINSA:
Hon. Abdulkadir Hassan (SLA) ya miƙa saƙon godiya ga mahalarta da masu goyon bayan gasar SLA Renewed Hope Football Competition.

Hon. Abdulkadir Hassan (SLA) ya bayyana matuƙar godiyarsa ga manyan baƙi, jami’an tsaro, jami’an Red Cross da ma’aikatan lafiya, masu sharhi kan wasanni, ‘yan wasa, magoya baya da kuma al’ummar da s**a halarci bikin buɗe gasar.

Ya ce goyon baya da halartar jama’a sun ƙara wa gasar armashi tare da nuna muhimmancin haɗin kai, bunƙasa matasa da kuma kishin wasanni.

Ya kuma yi fatan samun ci gaba da goyon bayan jama’a har zuwa ƙarshen gasar.
22 ga Agusta, 2026.

DA DUMI-DUMINSAHOTUNA: Yadda aka tarbi Maryam Ibrahim Dan Azumi, gwarzuwar gasar karatun Alƙur’ani ta ɓangaren mata da a...
22/08/2026

DA DUMI-DUMINSA

HOTUNA: Yadda aka tarbi Maryam Ibrahim Dan Azumi, gwarzuwar gasar karatun Alƙur’ani ta ɓangaren mata da aka gudanar a Birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, bayan dawowarta Najeriya.

Allah Ya ƙara mata basira da ɗaukaka. Amin.

DA DUMI-DUMINSÀ: HON. SADEEQ PLAZA YA BA DA TALLAFIN ₦200,000 GA G.S.S. A/ROGOHon. Sadeeq Plaza, ɗan takarar APC na Maja...
22/08/2026

DA DUMI-DUMINSÀ: HON. SADEEQ PLAZA YA BA DA TALLAFIN ₦200,000 GA G.S.S. A/ROGO

Hon. Sadeeq Plaza, ɗan takarar APC na Majalisar Tarayya mai wakiltar Bassa/Jos North, ya bayar da tallafin ₦200,000 (Naira Dubu Dari Biyu) ga Government Secondary School, Anguwan Rogo.

An miƙa tallafin ne a yayin bikin yaye ɗalibai na shekara-shekara na makarantar, domin tallafa wa ƙoƙarin makarantar na samar da ingantaccen yanayin koyo ga ɗalibai.

DA DUMI-DUMINSА: SHUGABANNIN JIBWIS SUN ISA BABBAR MASALLACIN LONDONHotuna: Lokacin da shugaban , tare da Sakataren Ƙung...
21/08/2026

DA DUMI-DUMINSА: SHUGABANNIN JIBWIS SUN ISA BABBAR MASALLACIN LONDON

Hotuna: Lokacin da shugaban , tare da Sakataren Ƙungiyar, , s**a isa babban masallacin da ke birnin London, inda shugaban ya jagoranci hudubar Sallar Juma’a da kuma sallar Juma’a.

Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sanya albarka. Amin.

Aliyu JTown
Hikima Multimedia TV Ltd

Address

Bauchi Roud Jos
Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hikima multimedia tv LTD posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share