11/06/2026
Kotu ta amince cewa Hausawan da aka haifa a Jos North suna da haƙƙin a ɗauke su a matsayin ’yan asalin yankin.”
Karin Bayani
Rahotanni sun nuna cewa wata kotu a Plateau ta yanke hukuncin da ya shafi matsayin Hausawan da aka haifa kuma s**a taso a Jos North, inda ta bayyana cewa ba za a ci gaba da nuna musu wariya ba wajen batutuwan da s**a shafi zama ’yan asalin yankin. Hukuncin ya taɓo muhawarar da aka daɗe ana yi a Jos kan bambancin “ɗan asali (indigene)” da “mazaunin gari (settler)”.
Wannan hukunci na iya yin tasiri wajen damar samun aiki, ilimi, muk**an gwamnati da sauran haƙƙoƙin jama'a ga Hausawan da aka haifa a Jos North. Ana kallonsa a matsayin wani muhimmin mataki a tattaunawar zaman lafiya da haɗin kai a Plateau.
:::